Mutum miliyan 1.6 aka yi wa rigakafin COVID-19 a Najeriya
Ana ci gaba da lissafa adadin mutanen da ke karbar rigakafin COVID-19.
Gwamnatin Tarayya ta ce sama da mutum miliyan 1.6 ne aka yi allurar rigakafin COVID-19, tun daga lokacin da aka fara allurar rigakafin a fadin Najeriya.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dokta Faisal Shuaib, ne ya bayyana hakan a wani taron kara wa juna sani na Kwamitin Shugaban Kasa (PSC), a ranar Litinin.
- Direba ya kashe jami’in KAROTA a Kano
- Majalisar Kano ta ba Ganduje awa 48 ya kori shugaban hukumar haraji
Shuaib ya ce mutum 1,692,315 sun karbi alluran rigakafin COVID-19 na Oxford-AstraZeneca, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince.
Ya kuma ce daga yammacin ranar Litinin an samu karin mutum 4,052,756 da suka karbi kashi na farko na allurar.
“Wannan ya kunshi mutum 2,645,020 da suka karbi na kashin farko na allurar AstraZeneca da mutum 1,407,736 da suka karbi kashin farko na allurar Moderna.
“Hakan ya kawo yawan wadanda aka yi wa allurar ya kai kimamin mutum miliyan 1.6,” inji Shuaib.
Ya ce an umarci jihohi da kada su karar da allurar Moderna don tanadin kashi na biyu na allurar.
Amma ya ce an fi so jihohin su mai da hankali wajen yi wa mutane rigakafin allurar kamfanin Astra-Zeneca.
Sannan ya bukaci jihohin da ba su bayyana wuraren da ake karbar allurar rigakafin ba da su yi kokarin yin hakan ta hanyar amfani da kafafen watsa labarai da kafofin sa da zumunta.
Sai dai ya yi karin haske cewa jihohi ne ke da alhakin adana da kare allurar rigakafin COVID-19 din da kuma katunan wadanda aka yi wa rigakafin, wadanda gwamnati ta aike musu.