Mutum miliyan 1 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka

Yawan mutanen da suka rasu sakamakon cutar COVID-19 a kasar Amurka ya haura miliyan daya a ranar Laraba.

Mutum miliyan 1 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka

Yawan mutanen da suka rasu sakamakon cutar COVID-19 a kasar Amurka ya haura miliyan daya a ranar Laraba.

Yawan mutanen da kafar talabijin ta Amurka, NBC News ta fitar ya haura na mazauna birnin San Jose da ke Jihar California — birni na 10 mafi girma a Amurka — bayan wata 27 da cutar ta fara bulla a kasar.

“Wadanda sauka kuma da cutar sun harbi daruruwan mutane, shi ya sa abin ke ta ninkuwa a tsakanin mutanen da ke yawo suna baza kwayar cutar,” inji Diana Ordonez, wadda mijinta mai shekara 40, Juan Ordonez, ya rasu a sakamakon cutar a watan Afrilun 2020.

A baya-bayan nan, alkaluman cutar ta COVID-19 sun nuna mutum 360 ke rasuwa kullum a sakamakon cutar a fadin kasar Amurka.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ana samun raguwar masu kamuwa da COVID-19 da kuma wadanda take kashewa, amma nau’in cutar na omicron na karuwa a yankin Amurka da kasashen Afirka.

A ranar Talata Hukumar Yaki da Cututtuka ta Amuraka (CDC) ta shawarci matafiya da su ci gaba da sanya takunkumi a cikin ababen hawa da wuraren taruwar jama’a, duk da cewa a ranar 18 ga Afrilu, kotu ta haramta dokar sanya takunkumi.

Amma CDC ta ce ta bayar da shawarar sanya takunkumin ne saboda muhimmancinsa wajen bayar da kariya da kuma hana yaduwar cutar.

Hakazalika Ma’aikatar Shari’ar kasar ta ce kafin ranar 31 ga watan Mayun da muke ciki za ta daukaka kara kan haramta dokar wajabta sanya takunkumi.