Mutum miliyan 8 ne suka ziyarci Masallacin Harami a goman farko

Akalla mutum miliyan takwas ne suka ziyarci Masallacin Harami da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya, a kwanakin 10 farko na watan azumin Ramadan din bana, kamar yadda ma’aikatar da ke aikin haji da umarah ta kasar ta bayyana. Wannan yana nufin cewa an samu karin masu ibada da kusan kashi 49 da cikin 100 […]

Mutum miliyan 8 ne suka ziyarci Masallacin Harami a goman farko
Mutum miliyan 8 ne suka ziyarci Masallacin Harami a goman farko

Akalla mutum miliyan takwas ne suka ziyarci Masallacin Harami da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya, a kwanakin 10 farko na watan azumin Ramadan din bana, kamar yadda ma’aikatar da ke aikin haji da umarah ta kasar ta bayyana.

Wannan yana nufin cewa an samu karin masu ibada da kusan kashi 49 da cikin 100 daga azumin bara, kamar yadda daraktan hukumar Dokta Salah Sakr ya bayyana.
Ya ce ana amfani da akalla motocin sufuri guda dubu uku da 800 wajen kaiwa da komowar masu ibada daga matsuguninsu zuwa masallacin a kullum. Hakazalika, wannan yana nufin cewa an samu karin kashi 25 daga yawan wadanda aka yi amfani da su a bara. Har ila yau, an kuma bude sabbin tashoshin mota guda takwas.
Dangane da sabbin gyare-gyaren da aka wa masallacin a bana, ya ce: “An sanya manyan talabijin din bango guda shida a ciki da harabar masallacin domin kallon sallah da kuma watsa sanarwa a harsuna daban-daban.”
Fiye da kofofi 160 ne ake budewa a kullum domin isa cikin masallacin mai hawa hudu. Hakazalika, akwai shinfidu da suka kai dubu 17 da kujerun guragu guda dubu 10, wadanda tsofaffi marasa karfi da kuma wasu marasa lafiya ke amfani da su, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Mutum miliyan daya ne da dubu dari biyu suka halarci sallar Juma’ar makon jiya, wadda ita ce ta biyu a Ramadan.