Mutum miliyan biyar na fama da cutar yanar ido
Mataimakin Shugaban Sashin Kula da Cututtukan da ba a fiye damuwa da su ba a Jihar Sakkwato, Alhaji Muhammad Hadi ya ce kimanin mutum miliyan biyar ne ke fama da cutar amosanin ido a sassan kasar nan. Alhaji Muhammad Hadi ya bayyana haka ne a wurin wani taron kara wa juna sani na wuni daya […]
Mataimakin Shugaban Sashin Kula da Cututtukan da ba a fiye damuwa da su ba a Jihar Sakkwato, Alhaji Muhammad Hadi ya ce kimanin mutum miliyan biyar ne ke fama da cutar amosanin ido a sassan kasar nan.
Alhaji Muhammad Hadi ya bayyana haka ne a wurin wani taron kara wa juna sani na wuni daya da aka shirya wa manema labarai a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce, ana fama irin wannan ciwo a kananan hukumomi takwas a jihar da suka hada da Wamakko da Silame da Bodinga da Gwadabawa da Kware da Isa da Sabon Birni da Rabah da Goronyo da Gada da Ilela da Binji da kuma Tangaza.
Ya ce jami’an lafiya na kasashen waje da hadin gwiwar gwamnatin jihar na kokarin kawar da cutar ta hanyar raba magani kyauta ga marasa lafiya, don daukar matakin ceto mutane daga makancewa.
Ya ce sauran cututtukan da suke addabar al’ummar jihar sun hada da tsutsar ciki da fitsarin jini, inda a bara a wata makaranta a garin Yabo aka gano dalibai 140 daga cikin 160 da ke karatu a makarantar na fama da cutar fitsarin jini, yayin da ake fama da cutar tsusar ciki a kananan hukumomi 20 da ke jihar.
Mataimakin Shugaban ya ce akwai bukatar sarakuna da malamai da ’yan jarida su taimaka wurin wayar da kan jama’a kan kula da tsabtar muhalli da jiki, domin galibin cututtukan da suke addabar jama’a suna da alaka da rashin tsabta.