Mutum miliyan uku sun rasa muhallinsu a Iraki
Fiye da mutum miliyan uku ne suka rasa muhallinsu a Iraki bayan da suka gudu daga gidajensu tun lokacin kungiyar ISIS ta kaddamar da yaki a kasar a shekarar 2014. Hukumar Kula da kaurar Jama’a ta Duniya (IOM) ta ce galibin wadanda suka fice daga gidajensu a Lardin Anbar da ke yammacin Bagadaza suke, saboda […]
Fiye da mutum miliyan uku ne suka rasa muhallinsu a Iraki bayan da suka gudu daga gidajensu tun lokacin kungiyar ISIS ta kaddamar da yaki a kasar a shekarar 2014.
Hukumar Kula da kaurar Jama’a ta Duniya (IOM) ta ce galibin wadanda suka fice daga gidajensu a Lardin Anbar da ke yammacin Bagadaza suke, saboda kungiyar ISIS ta kwace daukacin yankin.
Kusan mutum dubu 300 ne aka tilasta wa barin gidajensu cikin wata biyu a bana, bayan da kungiyar ta kwace iko da garin Ramadi.
Hukumar IOM ta ce fiye da mutum miliyan biyu na samun mafaka a gidajen jama’a, yayin da wasu fiye da dubu 600 suka zaune a sansanonin ’yan gudun hijira.
Wannan bayani yana zuwa ne a daidai lokacin da mayakan ISIS suka bukaci Musulmi su kaddamar da jihadi domin mutuwar shahada a cikin wannan wata na Azumin Ramadan. Kakakin kungiyar Abu Muhammad al Adnani ne ya yi wannan kira a cikin wani sako ta Intanet.
Adnani ya sanar da yin afuwa ga mutanen da ke yaki da su a Lardin Anbar na Iraki tare da yin kira ga wadanda suka gudu su dawo gidajensu.
Adnani ya ce jihadi kawai ke sa mutum kusanci da Allah, saboda haka yana kira ga magoya bayansu su gagaguta jihadi a cikin watan Ramadan.
Mayakan ISIS sun karbe iko da garuruwa da dama a Iraki tun lokacin da suka kaddamar da yaki a watan Yunin bara.