Mutum tara aka kashe a rikicin kabilanci a Jihar Ebonyi
Har yanzu al’ummar Ukwagba Ngbo, da ke Karamar Hukumar Ohaukwu ta Jihar Ebonyi na zaman makoki da dakon abin da hukuma za ta yi ga ’yan ta’addan da suka kashe musu mutum tara tare da jawo bacewar wadansu hudu a karshen makon jiya lokacin da rikici ya barke a yankin. Wannan lamari ya bakanta wa […]
Har yanzu al’ummar Ukwagba Ngbo, da ke Karamar Hukumar Ohaukwu ta Jihar Ebonyi na zaman makoki da dakon abin da hukuma za ta yi ga ’yan ta’addan da suka kashe musu mutum tara tare da jawo bacewar wadansu hudu a karshen makon jiya lokacin da rikici ya barke a yankin.
Wannan lamari ya bakanta wa Gwamnan Jihar Dabid Umahi rai matuka inda ya bayar da umarni a zakulo wadanda suka haddasa fadan da kuma makasan. Gwamnan ya bayar da umarnin ne lokacin da ya ziyarci hedkwatar Karamar Hukumar Ohaukwu.
Gwamnan wanda Mataimakinsa Barista Kelechi Igwe ya wakilta, ya ce, “Gwamnati bata jin dadin abin da ya faru ba a wannan karamar hukuma kuma abin kunya ne a ce Karamar Hukumar da tsohon Gwamnan Jihar Mista Sam Egwu ya fito wanda yanzu Sanata ne shi a ce irin haka ya faru a mazabarsa.”
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Kun ji kunya a ce koyaushe al’ummar Agila kuna kashe junanku, kun mayar da rai tamkar na kiyashi,” inji shi.
Bayan Gwamnan ya gama jawabi an rubuta takardar yarjejeniya a tsakanin gwamnati da al’ummar yankin kan zaman lafiya kuma gwamnatin ta bukace su da su tabbabar sun zakulo makasan da masu ruruta wutar rikicin a yankin. “Ku tabbatar kun gano wadanda suka haddasa rikicin da kuma wadanda suka aikata kisan mutum tara da wadanda suka bace ba a gansu ba, domin gwamnati ba za ta kyale ku ba ana ci gaba da mayar da rayukan jama’a kamar na kiyashi,” inji Gwamnan.