Mutum tara sun halaka a fafatawa da mahara a Zamfara
A daren Lahadin da ya gabata ne kimanin mutum tara suka rasa rayukansu a wata arangama da ta gudana tsakanin wadanda ake zargin barayi ne da suka kai hari a kauyen Gobirawan Fulani da ke masarautar dansadau a Jihar Zamfara.Majiyarmu ta ce da misalin karfe 9:00 na dare ne mazauna kauyen suna zaune sai suka […]

A daren Lahadin da ya gabata ne kimanin mutum tara suka rasa rayukansu a wata arangama da ta gudana tsakanin wadanda ake zargin barayi ne da suka kai hari a kauyen Gobirawan Fulani da ke masarautar dansadau a Jihar Zamfara.
Majiyarmu ta ce da misalin karfe 9:00 na dare ne mazauna kauyen suna zaune sai suka samu labarin barayin sun nufo kauyen nan take mazaje suka dauki matakin kare kansu daga barayin kuma cikin kankanen lokaci dai sai aka shiga ba ta kashi inda mutum
biyar daga jama’ar kauyen suka rasu hudu kuma daga bangaren maharan, sannan sam da mutum bakwai da suka samu munanan raunuka suna kwance a asibitin garin Magami.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa jama’ar kauyen sun yanke shawarar daukar matakin kare kansu ne saboda sun amince da maganganun da Sanata dansadau ya yi cewa babu wanda zai iya kare su a yanzu.
Majiyar ta ce mazauna kauyen ba su samun yin barci na tsawon lokaci ba, kuma sun yi kwanton bauna wa maharan ne lokacin da suka samu labarin za su auka wa suka kauyen, inda barayin na shigowa, suka shiga dauki babu dadi.
Sai abin bai tsaya ga Gobirawa kawai ba, domin a wani kauye da ake kira Kangon Gabas a fafata tsakanin barayin da sojoji kuma an kashe wasu daga cikin maharan, sai dai jama’a sun kaurace wa kauyen suka koma garin Magami suka kwana.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara DSP Lawal Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya shaida wa manema labarai cewa suna gunanar da bincike, kuma sun tura mutanensu kauyukan. Ya roki jama su kwantar da hankalinsu, kuma su kai rahoton wanda ba su amince da take-takensa ba.