Mutum tara sun mutu a hadarin mota shekaranjiya a Jihar Kuros Riba
A kalla mutum tara ake kyautata zaton suka mutu shekaranjiya Labara a wani hadarin mota da ya rutsa da su lokacin da suka tashi daga Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Rriba zuwa jihohinsu na asali da ke arewacin Nijeriya.Hadarin motar, kamar yadda wani jami’in hukumar kare hadurra (FRSC), wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya […]
A kalla mutum tara ake kyautata zaton suka mutu shekaranjiya Labara a wani hadarin mota da ya rutsa da su lokacin da suka tashi daga Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Rriba zuwa jihohinsu na asali da ke arewacin Nijeriya.
Hadarin motar, kamar yadda wani jami’in hukumar kare hadurra (FRSC), wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiyia cewa motar da mamatan suke ciki ce ta yi karon taho-mu-hada da wata mota kirar bas, irin wadda suke ciki, a daidai wata mahada da ke karamar Hukumar Biase.
Mamatan, wadanda ’yan asalin jihohin Sakkwato da Zamfara ne, har ma ana kyautata zato da wani dan asalin jamhuriyar Nijar, sun kama hanya ce zuwa gida domin ganin iyalansu, ajali ne ya yi kira, suka rasa rayukansu.
Alhaji Hashimu Sakkwato, shugaban kungiyar ’yan asalin jihar, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya ce, “Lokacin su ne ya yi, muna fata Allah Ya jikansu”.
Shi ma Alhaji Haruna, dan uwan wani mamaci mai suna dayyabu, ya bayyana wa Aminiya cewa, “Jiya (Talata) yaron nan ya zo wurina ya sayi jakar sa kaya, wadda ake cewa ‘Ghana-must-go’ ya ce min shi ya gaji da neman kudin nan, bari ya tafi gida ya huta, idan an kwana biyu ya dawo, kwatsam da safe sai na ji kiran waya ana ce min ai dayyabu sun yi hadari ya mutu”.
Tuni aka yi jana’izarsu. Sauran wadanda suka jikkata kuma suna karbar magani a asibitin Ugep.