Mutum uku da aka ce suna neman kujerar Minista daga Jihar Nasarawa

Jim kadan da rantsar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, wadansu jiga-jigan Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa suka soma nuna sha’awarsu ta neman kujerar wanda zai wakilci jihar a Majalisar Zartarwa ta Kasa a matsayin Minista.                                                                                                                                             Doka ta ba Shugaban Kasa damar nada Minista daya daga kowace jiha daga cikin jihohi 36 […]

Mutum uku da aka ce suna neman kujerar Minista daga Jihar Nasarawa

Jim kadan da rantsar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, wadansu jiga-jigan Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa suka soma nuna sha’awarsu ta neman kujerar wanda zai wakilci jihar a Majalisar Zartarwa ta Kasa a matsayin Minista.                                                                                                                                             Doka ta ba Shugaban Kasa damar nada Minista daya daga kowace jiha daga cikin jihohi 36 na kasar nan. A Jihar Nasarawa wakilinmu ya gano cewa neman mukamin ya zafara a tsakanin jiga-jigan Jam’iyyar APC idan aka yi la’akari da yadda wadanda ke da sha’awar mukamin suka fara tuntubar wadanda suke ganin za su iya taimaka musu su samu shiga. Wata majiya ya bayyana wa wakilinmu cewa wadanda ke neman kujerar sun dogara ne da kusancinsu ga Shugaba Buhari ko Jam’iyyar APC ta Kasa, duk da cewa Shugaban Kasar ya nanata cewa a karon nan zai yi nadinsa ne bisa cancanta ba bisa kasancewa mamban jam’iyyarsa ko gudunmawa ga jam’iyya ba. Wadanda aka ce suna sha’awar zama Minista daga jihar sun hada da Alhaji Ahmed Aliyu Wadada da  Mista Silas Agara da Injiniya Idris Wada.

 Ahmed Aliyu Wadada:

Kwararru a fannin siyasar jihar suna ganin shi ne mafi farin jini a cikin wadanda ke neman kujerar. Yana daya daga cikin ’ya’yan Jam’iyyar APC 11 da suka fafata a zaben fidda-gwani na Jam’iyyar APC wanda Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule, shi kuma Aliyu Wadada ya zo na biyu. Bayan  hakan ne kuma ya  jagoracin kwamitin kamfen din Gwamna Abdullahi Sule, inda aka ce ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan ’ya’yan jam’iyyar da suka nemi kujerar don tabbatar da nasarar  Gwamna Abdullahi Sule da jam’iyyar a jihar da kasa baki daya. Kuma wannan ne karo na farko da Shugaba Buhari ya lashe zabe a jihar. Tsohon dan Majalisar Wakilai daga mazabar Keffi da Karu da Kokona a a shekarar 2003 zuwa 2011, Wadada ya fito takarar Sanata Nasarawa ta Yamma a shekarar 2015 a Jam’iyyar PDP inda ya kusan kada Sanata Abdullahi Adamu na Jam’iyyar APC. Wadansu dai na ganinsa a matsayin dan siyasa da ya fi farin jini da karbuwa a wurin al’ummar jihar cikin masu neman zama Minista daga jihar.

 Salas Ali Agara:

Shi ma dan Jam’iyyar APC ne mai matukar biyayya ga jam’iyyar. Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar ne wanda Shugaban Jam’iyyar na Kasa Adams Oshiomhole ya taba kwatanta shi da mafi biyayya da rikon amana a cikin dukkan mataimakan gwamnoni a tarihin siyasar kasar nan. Ya yi aiki da duk gwamnonin farar hula 3 da suka jagoranci jihar ba tare da an same shi da wata matsala ba. Mataimakin tsohon Gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura, Agara ya zo na uku a zaben fidda-gwani na APC, kuma ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar. A lokacin da ya fadi zaben fidda gwanin jama’a da dama sun dauka zai canja sheka zuwa wata jam’iyya. Amma ya zauna a jam’iyyar har ya kai ga jam’iyyar  ta APC ta yi nasara karo na farko a karamar hukumarsa ta Akwanga. Ya kuma kasance Shugaban Kwamitin Karbar Mulki daga tsohon Gwamna Umaru Tanko Al-Makura zuwa ga Gwamna Abdullahi Sule. Wadansu na ganin zai iya yin amfani da ubangidansa tsohon Gwamna Umaru Tanko Al-Makura wajen samun mukamin.

 Injiniya Idris Wada:

Tsohon Kwamishinan Ayyuka ne a gwamnatin Umaru Al-Makura da ta gabata. Ya rike wannan mukamin tun farkon gwamnatin Al-Makura har zuwa karshenta kafin ya sauka  don ya nemi kujerar dan Majalisar Dokokin Jihar. Wakilinmu ya ce akwai jita-jitar da ke yaduwa a jihar a yanzu cewa shi ne wanda tuni Shugaban Kasa ya riga ya zaba a matsayin wanda zai nada Minista. Ana kuma zargin cewa wadansu na kusa da Shugaban Kasa suna shawartarsa ya nada Injiniya Idris Wada, Ministan Abuja don ya aiwatar da irin shirin tsohon Gwamna Al-Makura na gina karamin birnin don tsara Birnin Tarayya ,Abuja yadda ya dace. Masu wannan ra’ayi sun ce jam’iyyarsa ta APC a jihar tare da ubangidansa Sanata Umaru Al-Makura za su iya yin duk mai yuwa don tabbatar an saka masa da kujerar Minista tunda ya fadi a zaben gama-gari don wakiltar mazabarsa ta Keffi a Majalisar Jihar.