Mutum uku sun mutu ana ruwan sama da iska a Yobe

Lamarin, wanda ya faru cikin dare ya shafi unguwannin Tsohon Nguru, Filin Idi da wasu yankuna, inda gidaje da shaguna da rumfunan kasuwa da katanga suka rushe, tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira.

Mutum uku sun mutu ana ruwan sama da iska a Yobe

Aƙalla mutum uku ne aka tabbatar da sun rasu, yayin da ɗaruruwan mutane suka rasa muhallansu bayan ruwan sama mai ƙarfi tare da iska ya haddasa mummunar ɓarna a ƙaramar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe.

Lamarin, wanda ya faru cikin dare ya shafi unguwannin Tsohon Nguru, Filin Idi da wasu yankuna inda gidaje da shaguna da rumfunan kasuwa da katanga suka rushe, tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira.

Wani mazaunin yankin, Bukar Adamu ya ce iyalan da lamarin ya shafa sun tsere zuwa gidajen ’yan uwa da wasu gine-ginen gwamnati saboda gidajensu sun lalace.

Shi ma wani mazaunin yankin, Mustapha Modu ya ce iska ta ɗauke rufin gidansa, yayin da wani yaro mai suna Ilya Alhassan ya rasu bayan ɗaki ya rufta masa a unguwar Filin Idi.

A halin yanzu, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA) ta fara tantance irin ɓarnar da aka yi domin gwamnati ta kai wa waɗanda abin ya shafa agajin gaggawa.

Mutum uku sun mutu ana ruwan sama da iska a Yobe

An ceto mutane da aka sace da ƙwato dabbobi a Katsina 

Dalilan da ya sa Gwamnonin APC suka ziyarce ni — Jagoran ADC

Iyayen Mary Habila sun ce a ba su gawarta don binne ta

Tags