Mutumin da aka haifa da kai a jirkice ya zama Akanta

Wani mutum mai suna, Claudio bieira de Olibeira  wanda aka haifa da wata cutar gabobin jiki, wadda kuma ta jirkitar masa da kansa, ya zama Akanta, bayan likitoci sun shaida wa mahaifiyarsa cewa ba zai rayu ba, lokacin da ta haife shi kimanin shekara 37 da suka wuce.Kamar yadda jaridar Daily Mail da ke Birtaniya […]

Mutumin da aka haifa da kai a jirkice ya zama Akanta
Mutumin da aka haifa da kai a jirkice ya zama Akanta

Wani mutum mai suna, Claudio bieira de Olibeira  wanda aka haifa da wata cutar gabobin jiki, wadda kuma ta jirkitar masa da kansa, ya zama Akanta, bayan likitoci sun shaida wa mahaifiyarsa cewa ba zai rayu ba, lokacin da ta haife shi kimanin shekara 37 da suka wuce.
Kamar yadda jaridar Daily Mail da ke Birtaniya ta bayyana, Mista Claudio wanda a bana ya kammala karatun aikin Akanta, yana zaune ne a garin Monte Santo da ke kasar Brazil, kuma kwararre wajen iya magana a bainar jama’a.
Kodayake  a lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi da larurar, likitoci sun ba ta shawarar cewa ta bar shi ya mutu da yunwa domin ba zai rayu ba, amma sai ta yi biris ta ci gaba da ba shi kulawar da ta kamata. Sai dai a cewarta “ban ta taba tunanin cewa zai rasu har ya kawo yanzu ba,”
Ta ci gaba da cewa: “Musamman saboda yadda yake  numfashi sama-sama a lokacin. Wasu ma cewa suke ka da na dinga ba shi abinci saboda mutuwa zai yi. Amma sai yanzu ne farin ciki ya zo mana, Claudio mutum ne kamar kowa. Ba ya bukatar wani taimako daga wurin kowa, ya fi so ya yi komai da kansa kamar yadda kowa kan yi. Hakan ya karfafa masa gwiwa gaya. Ba ya jin kunyar yawo a gari, bil-hasani ma, za ka ga yana yawo ne – yana rera waka, yana rausayawa,” inji ta.
Da yake bayyana yadda kuruciyarsa ta kasance, Mista Claudio, ya ce: “Tun lokacin da nake yaro, ni yaro ne mai son aikace-aikace, na tsani zama. Ko a yanzu da kaina nake kunna talabijin da rediyo da daukar wayata ta hannu da kuma amfani da na’urar kwamfuta. Ba tare da neman wani agaji daga wurin kowa ba,” inji shi.
Yana yin rubutu ne ta hanyar sanya abun rubutun a baka. Yana kuma sarrafa wayar salularsa da na’urar kwamfuta ta amfani da labbansa, sai dai idan zai fita zuwa wani guri, yana amfani ne da wasu takalman musamman.
Ana ganin kasancewarsa mai dogaro da kansa a kodayaushe, ya taimaka masa sosai wajen samun gurbin karatun Akanta a Jami’ar  Feira de Santana da ke kasar ta Brazil.
A lokacin da ya kai shekara takwas ne ya fara tafiya da gwiwa, amma kafin hakan ana daukarsa ne a hannu duk inda zai je.  A wancan  lokacin  sai da ta kai da  an canza dabem gidansu baki daya don ya dace da shi, gudun kar ya dinga samun rauni. Hakazalika, makunnan fitilun wutar lantarkin dakinsa duka, sai da aka dawo da su kasa-kasa saboda ya iya amfani da su ba tare da neman taimakon wani ba.
Har ila yau, wani kalubale da Mista Claudio ke fuskanta  shi ne, ba zai iya amfani da keken guragu ba domin yadda surar jikinsa ta fita daban da ta masu amfani da keken, wannan ya sa yana matsaloli sosai idan ya fita gida. Kodayake, duk da haka ya roki mahaifiyarsa alfarmar ta bar shi da ya je makaranta domin yin karatu da takwarorinsa dalibai.
A lokacin da likitoci suka kammala bincike sun ce yana fama ne da wata cuta mai suna, Congenital Arthrogryposis, wadda take hana gabobinsa aiki kwata-kwata .
Mista Claudio ya ce: ‘’A duk tsawon rayuwata ina kokari ne na ga yadda jikina zai daidaita don ya dace da wannan duniyar. A yanzu ba na ganin kaina daban da sauran mutane.  Ni mutum ne kamar kowa. Kuma ba na ganin abubuwa a jirkice, wannan yana ba mutane mamaki  matuka a duk lokacin da bayyana masu hakan.”
Ya ci gaba da cewa : “’Amma mu’amalata da jama’a a yanzu tana zuwa ne cikin sauki. Ba na tsoron kowa kuma zan iya bugun kirji na ce ni kwararre ne wajen iya magana a gaban jama’a. Kuma ana gayyatana aiki daga ko ina a fadin duniya,” inji shi.