Mutumin da aka yi wa dashen zuciyar alade ya mutu
Ya rayu na tsawon wata biyu bayan dashen zuciyar alade.
David Bennett, mutumin nan na farko da aka yi wa dashen zuciyar alade a duniya ya mutu.
Bennett, wanda ke fama da ciwon zuciya da ya kai makura ya rayu na tsawon wata biyu bayan dashen zuciyar alade da aka yi masa a Amurka.
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 19 a Kebbi
- Birtaniya ta kwace jirgin saman attajiri dan kasar Rasha
Amma rashin lafiyar ta fara tsananta a kwanakin da suka gabata, kamar yadda likitansa Baltimore ya bayyana.
Ya ce David Bennett mai shekara 57 ya mutu ne a ranar Litinin 8 ga watan Maris.
A watan Janairun da ya gabata ne Aminiya ta ruwaito yadda Bennett da aka yi wa dashen zuciyar alade ya bayyana dalilinsa na amincewa, duk cewa ya san akwai hatsari a tattare da yin hakan.
Likitoci a kasar Amurka ne suka yi nasarar yi wa mutumin mai suna David Bennett mai mai shekara 57 dashen zuciyar alade da aka sauya kwayar halittarta a karon farko a tarihi.
An sanar da hakan bayan likitocin sun kammala aikin dashen zuciyar a Asibitin Koyon Aikin Likita na Jami’ar Marylanda da ke Kasar Amurka.
Karon farko ke nan a tarihi da aka gudanar da irin wannan aiki cikin nasara a wani yunkuri na shawo kan matsalar karancin masu bayar da gudunmawa, domin ceton rayukan masu fama a matsalar zuciya.
Sanarwar da aka fitar ta ce bayan aikin da ya gudana cikin nasara, an kafa sabon tarihi a fannin yi wa dan Adam dashen sassan jikin dabba.
Ta bayyana cewa an yi wa wani mara lafiyan mai suna David Bennett, dashen zuciyar aladen na bayan gwajin da aka yi masa ya nuna jikinsa ba zai iya daukar dashen zuciyar dan Adam ba, saboda wasu cututtuka da ya jima yana fama da su.
Dole na zabi a yi min —Bennett
A halin yanzu Mista Bennett yana murmurewa kuma ana ci gaba da kula da shi a asibitin tun bayan an kammala aikin tiyatar da aka yi masa.
“Ba ni da wani zabi face in yarda a yi min wannan dashen ko kuma a bari in mutu. Ni kuma so nake in rayu.
“Na san akwai tsabar kasada, amma ba ni da wani zabi da ya wuce hakan,” inji Mista Brennett, kafin a shigar da shi dakin tiyata.
A watan Nuwambar bara ce Aminiya ta ruwaito cewa, a karon farko wani kwararre a fannin tiyata a Amurka mai suna Dokta Robert Montgomery ya ce, sun samu nasarar dasa wa wani mutum kodar alade, inda suke fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen karancin taimakon koda da ake samu a wannan lokaci.