Mutumin da ake zargi da kisan kai ya shiga hannu bayan shekara 39

Mista Santini ya shiga wasan buya da jami’an tsaro bayan kashe matar a Jihar Florida ta Amurka a shekarar 1984.

Mutumin da ake zargi da kisan kai ya shiga hannu bayan shekara 39

Donald Santini da Cynthia Woods

Hukumomi a Amurka sun kama mutumin da ake zargi da aikata kisan kai bayan kusan shekara 40 yana wasan buya da jami’an tsaro.

’Yan sanda sun ce ana zargin Donald Santini mai shekara 65 da amfani da sunayen karya 13 domin kauce wa kamun jami’an tsaro bayan kashe wata mata mai shekara 33 a Jihar Florida ta Amurka a shekarar 1984.

An kama shi ne a yayin da yake aiki a matsayin shugaban hukumar ruwa a wata unguwa a Jihar California.

An dai tisa keyarsa zuwa Jihar Florida domin fuskantar tuhuma kan zarge-zargen da ake yi masa.

Hukumomin sun ce Mista Santini shi ne mutum na karshe da aka gani da matar mai suna Cynthia Woods kafin a tsinci gawarta daure cikin wata hanyar ruwa.

Hukumomin sun ce ya gudu daga yankin bayan da aka zarge shi da kashe matar.

An yi ta nuna hotunansa a gidajen talbijin na kasar a matsayin mutumin da ake nema ruwa-a-jallo a shekarun 1990, da 2005, da kuma 2013.

BBC

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan