Mutumin da ake zargi da yi wa ’yar shekara 2 fyade ya dora wa barasa alhaki

Mutumin yana da mata wadda a yanzu haka tana da juna biyu.

Mutumin da ake zargi da yi wa ’yar shekara 2 fyade ya dora wa barasa alhaki

Wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da yi wa ’yar shekara biyu fyade a Jihar Adamawa, ya dora alhakin ta’adar da ya aikata a kan barasa.

Mutumin mazaunin kauyen Aljannaru da ke Karamar Hukumar Song, ya shiga hannun jami’an ’yan sanda a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Sai dai mutumin a yayin shan titsiye, ya ce ya yi aika-aikar ne sanadiyyar mankas a dalilin barasa da ya yi tatul da ita.

A cewarsa, a ranar da lamarin ya faru, ya sha wata barasa mai suna Voltage, wadda ta jefa shi cikin yanayi na matsananciyar sha’awa da ya kasa jurewa har ya zakke wa karamar yarinyar.

Aminiya ta ruwaito cewa, wata yayar yarinyar ce ta kama shi yana tsaka da masha’a da kanwarta, lamarin da ya kai ga cafke shi kuma a mika shi hannun ’yan sanda.

A yayin bincike, an gano cewa mutumin magidanci ne da matarsa wadda a yanzu haka ma tana da juna biyu.

Tuni dai Kwamishinan ’Yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike a kan lamarin sannan a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo