Mutumin da ya auri jikarsa a Zamfara ya ki rabuwa da ita

Ya ce ya ji ya gani don kuwa shi da matarsa mutu-ka-raba takalmin kaza.

Mutumin da ya auri jikarsa a Zamfara ya ki rabuwa da ita

Wani magidanci, Alhaji Musa Tsafe mai shekaru 47, ya cije akan kin sakin jikarsa wadda ya aura shekaru 20 da suka gabata.

Mutumin wanda ke zaune a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara tare da iyalinsa, ya ce ba zai sawwakewa jikar tasa ba duk da an ankarar da shi a kan haramcin igiyar auren da aka kulla a tsakaninsa da ita.

Bayanai sun ce, matar mai suna Wasila Isah Tsafe mai kimanin shekaru 35, wadda jika ce ga babban yayan Alhaji Musa, ta haifa masa ’ya’ya takwas a tsawon shekaru 20 na aurensu.

Sai dai wannan lamari da ya dauki wani sabon salo, ya kara jefa rayuwar ma’auratan cikin rudani, inda ma’abota sani na addinin Islama suka sanar da Masarautar Tsafe kan haramcin auren.

Shugabannin al’umma da malaman addinin musulunci da suka gayyaci ma’auratan domin su binciki lamarin, sun gano cewa auren ya saba wa koyarwar addini.

Hakan ce ta sanya Malaman suka shawarci Alhaji Musa a kan ya saki matarsa ​​amma ya yi biris ya ce ba za ta sabu ba.

Wannan kuwa na zuwa ne duk da malaman sun halasta ’ya’yan da suka riga suka haifa, sai dai sun ce a yanzu da aka gano yadda lamarin yake, aure ya haramta a tsakaninsu.

Bayan ya kekashe ne aka mika lamarin zuwa Hukumar Hisbah da ke Karamar Hukumar Tsafe, wadda kuma nan da nan aka garzaya wata Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da a yanzu ta sanya 21 ga watan Yuli a matsayin ranar ci gaba da sauraron karar.

Ana tsaka da wannan takaddama ce, Alhaji Musa ya garzaya wajen Sheikh Dahiru Bauchi, yana mai koken cewa wannan wata kitimurmura ce ta neman a sanya tsare-tsaren akidar ’yan Izala a cikin lamarin aurensa.

Sai dai Shehun Malamin wanda shi ne jagoran Darikar Tijjaniya na Najeriya, ya tabbatar da maganar malaman ta cewa auren ya haramta, sai dai shi kuwa Alhaji Musa ya ce ya ji ya gani don kuwa shi da matarsa mutu-ka-raba.