Mutumin da ya bai wa matar da yake so kodarsa ta ki aurensa

Wani mutum a birnin Landan da ke kasar Birtaniya ya ceci rayuwar wata mata da yake soyayya da ita tsawon shekara 20, har y aba ta kyautar kodarsa aka yi mata dashe, amma ta ki amince da bukatarsa ta aurensa. Simon Louis mai shekara 49, ya bijiro da bukatarsa ga Mary Emmanuelle, mai shekara 41, […]

Mutumin da ya bai wa matar da yake so kodarsa ta ki aurensa

Wani mutum a birnin Landan da ke kasar Birtaniya ya ceci rayuwar wata mata da yake soyayya da ita tsawon shekara 20, har y aba ta kyautar kodarsa aka yi mata dashe, amma ta ki amince da bukatarsa ta aurensa. Simon Louis mai shekara 49, ya bijiro da bukatarsa ga Mary Emmanuelle, mai shekara 41, wadda t ayi fama da matsanancin ciwon koda, har ta yi suman tsawon makonni biyu kafin a yi mata dashe.

Masoyan sun hadu ne a Landan tsawon shekarun 1990, lokacin mary na ’yar shekarar 20,kuma Simon na da shekara 28. Duk da soyayyar da ke tsakaninsu, Mary ta yi watsi da bukatar Simon, saboda a cewarta makomarta ba ta da tabbas, bisa la’akari da raunin da jikinta ya yi saboda rashin lafiya, kamar yadda jaridar Mirror ta Landan ta ruwaito.

Sai dai masoyan sun amince su ci gaba da zama abokan juna, domin a cewar Simon: “Na ba ta kaunar zuciyata, amma sai na karke da da ba ta koda ta. Ko ma dai mene ne ya faru, ba zan yi nadamar wannan kyautar rayuwa da na ba ta ba.”

Ita kuwa Mary cewa ta yi: “shi ne mafi nagartar abokaina, kamar yadda zai kasance a kodayaushe. Domin yana iya rasa ransa kan wannan abin da ya ikata.”

A Satumbar 2014 Mary, wadda a lokacin take da shekara 37, kwatsam ta fadi rashe-rashe a gida,kuma fatar jikinta ta koma dorawa. danta Dwayne, lokacin yana da shekara 21, ya sameta kwance a daben daki tana tauna amanta, sai aka yi saurin kaita asibitin da ke Kudancin Landan. Ta yi fama da zubar jini a kwakwalwa, sannan ta suma, sai aka kaita, inda aka kaita sashen bai wa marasa lafiya cikakkiyar kulawa. Sai dai yanayin jininta da ya nuna alamar rukunin -B yana nuna matukar wahalar smaun wanda zai iya ba ta kyautar kodar da ta dace da ita. Don haka aka sallameta daga asibiti a Janairun 2015, amma dole aka rika yi mata aikin tace jinin koda.

Simon wanda yake a gefenta tsawon wancanlokacin, sai ya bukaci a gwada shi don ganin ko ya dace ya ba ta gudunmuwar. Abin mamaki sai kawai ya dace, don haka ya bai wa Mary kyautar kodarsa daya.

Watanni kadan bayan sun murmure daga aikin da aka yi musu, Simon y yi karfin hali a wani dare,lokacin da yake girkin abinci, ya gabatar da bukatarsa ta aure ga Mary. Mary ta ce: “Na yi matukar jin cewa ka kambama ni, cewakana son aurena, bayan da ka ganni a wannan mummunan hali.”

Duk da cewa Simon bai yi nadamar bayar da kodarsa, ya ce: “Ban yi wani nazarin kai-kawon tuni kan lamarin ba. Babu abin tuhuma kan yin wani abu (taimako) ga wanda kake so.”