Mutumin da ya fi kiba a Birtaniya ya rasu
Mutumin nan da ya fi kowa teba a Birtaniya ya rasu, ranar Lahadi, yana da shekara 33 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Guardian ta bayyana. Marigayin mai suna, Carl Thompson, wadda yake nauyin Kilogram 412, ya riga mu gidan gaskiya ne a safiyar ranar Lahadi a gidansa da ke garin Dober a yankin Kudu-maso-Gabashin […]
Mutumin nan da ya fi kowa teba a Birtaniya ya rasu, ranar Lahadi, yana da shekara 33 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Guardian ta bayyana.
Marigayin mai suna, Carl Thompson, wadda yake nauyin Kilogram 412, ya riga mu gidan gaskiya ne a safiyar ranar Lahadi a gidansa da ke garin Dober a yankin Kudu-maso-Gabashin kasar Ingila.
An ruwaito cewa sai da jami’an ’yan sanda da na kwana-kwana suka kwashe sa’o’i da dama, kafin su yi amfani da wata karamar katafila wajen cire gawarsa daga gidan.
Carl ya yi suna sosai ne a fadin kasar bayan da likitoci suna bukace shi da ya rage tebarsa da kimanin kashi 70 cikin 100. An bayyana cewa marigayin yana cin abin mutum hudu ne a kullum kafin, inda yake kashe Yuro 200 (kimanin naira dubu 47) a kowane mako. Har ila yau, an ce ba ya iya yin lafiya, wanka, sanya tufafi da sauran bukatun yau da kullum da kansa. A bara kawai, an ruwaito cewa ya samu bugun zuciya akalla sau biyar.