Mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya
Tsayin hancin Mehmet Özyürek ya kai inci uku da rabi.
An gano mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya, wanda tsawon hancinsa ya kai inci uku da rabi.
Shekara 10 ke nan bayan mutumin mai suna Mehmet Özyürek mai shekara 71 dan kasar Turkiyya ya fara shiga Kundin Tarihi na Guinness a matsayin wanda ya fi kowa tsawon hanci a shekarar 2010.
- Na kunyata kaina da iyalaina —Fani-Kayode
- Ganduje ya sake korar tsohon Kwamishinan da ya yi ’murna’ da mutuwar Abba Kyari
An fara tabbatar da tsayin hancin Mehmet ne bayan da ya bayyana a shirin wani gidan talabijin din na kasar Italiya, inda aka gwada tsayin karan hancin nasa aka samu ya kai sentimita 8.8, kamar yadda jaridar The Mirror ta rawaito.
“Tsayin hancin Mehmet ya kai sentimita 8 da digo 8 wanda ya yi daidai da inci uku da rabi, idan aka auna daga tsakanin idanunsa zuwa karshen karan hancinsa,” a cewar jaridar.
Tun a lokacin aka ba Mehmet lambar yabo na Kudin Tarihin Guiness kuma har zuwa yanzu ba a samu wanda ya doke shi wajen tsayin hanci ba.
– Wanda ya fi tsawon hanci a tarihi
Yanzu dai Mehmet Özyürek ya kare kambinsa na rayayyen mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya.
Amma mutumin da ya fi tsawon hanci a duniya a tarihi shi ne wani mai suna Thomas Wedders daga yankin Yorkshire na kasar Birtaniya.
Kundin Tarihi na Guiness ya nuna cewa tsawon hancin Wedders, wanda ya rayu a shekarun 1770, ya kai santimita 19 wato inci bakwai da rabi.
Saboda tsawon hancinsa, Wedders, wanda ke cikin ayarin wasu ’yan gambara kan zaga gari suna nuna wa mutane hancin nasa.