Mutumin da ya fi kowa yawan iyalai a duniya ya kwanta dama
Mai kimanin shekaru 76 a duniya, mutumin ya rasu ranar Lahadi ya bar mata 38 da ’ya’ya 89.
Mutumin nan dan kasar Indiya da aka yi ittifakin ya fi kowa yawan iyalai a duniya, Ziona Chana ya rasu.
Mai kimanin shekaru 76 a duniya, mutumin ya rasu ranar Lahadi ya bar mata 38 da ’ya’ya 89.
- Rabon mukamai: Buhari bai mayar da ’yan kabilar Ibo saniyar ware ba – Ngige
- ’Yan bindiga sun mamaye Zariya —Sarkin Zazzau
Mista Ziona dai shine yake jagoranci wata darika a addinin Kiristanci da ke goyon bayan auren mata da yawa.
An dai kafa darikar mai suna Chana Pawl, wacce ainihi mahaifinsa ne ya assasa ta a shekarar 1942, kuma tana da mabiya kimanin 2,000, akasarinsu mazauna kauyen Baktawangna da ke gundumar Mizoram a kasar ta Indiya.
A ranar Lahadi ne dai Babban Ministan gundumar Mizoram, Zoram Thanga ya sanar da rasuwar Ziona a shafin Twitter.
“Cikin yanayin alhini, gundumar Mizoram ta yi bankwana da Mista Ziona yana da kimanin shekara 76 a duniya, wanda aka yi ittifakin ya fi kowa yawan iyali a duniya, inda ya bar mata 38 da ’ya’ya 89,” inji shi.
Ministan ya kuma ce tuni garuruwan na Mizoram da Baktawang Tlangnuam suka kasance wasu cibiyoyin yawon bude ido saboda iyalan mamacin.
A cewar hukumomin, Mista Ziona, wanda kuma yake da jikoki 33 ya rasu ne sakamakon fama da ciyon suga da kuma hawan jini, kamar yadda kafafen watsa labaran kasar Indiya suka rawaito.
Ana dai ganin rasuwar tasa a matsayin wani babban rashi ga yankin.
Marigayin dai ya yi aurensa na fari ne a shekarar 1959, lokacin yana shekara 17, kuma ya taba auren har mata 10 a cikin shekara daya.
Ya auri matarsa ta karshe ne a shekarar 2004 inda ya auri wata mai shakara 25.
Mazauna yankin dai sun ce iyalan na zaune ne a wani katon gida mai hawa hudu da ke da dakuna 100, wanda ake kira da ‘New Generation Home’.
Galibi dai inji makwabtansa, mutumin ya kan so kamar mata bakwai zuwa takwas su kwanta a kusa da shi a cikin turakarsa.
A kasar Indiya dai doka ta haramta auren mata da yawa, ko da yake akwai wasu tsirarun kabilu a yankin Arewa maso Gabashin kasar da al’adunsu suka halatta auren, kuma dokar kasar ta amince da hakan.
To sai dai duk da yawan iyalan nasa, Mista Ziona ya taba shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters a shekarar 2011 cewa yana son ya ga ma sun fi haka yawa.