Mutumin da ya fi muni a Uganda ya samu karuwa

Mutumin nan da ya fi muni a kasar Uganda ya samu karuwar da namiji, inda yanzu ’ya’yansa suka kai takwas kamar yadda jaridar Metro ta ruwaito. Mutumin mai suna, Godfrey Baguma, wanda aka yi amannar cewa yana fama da ciwon tabun hankali, ya ce ya yi farin ciki matuka da samun labarin haihuwar mai dakinsa.Godfrey […]

Mutumin da ya fi muni a Uganda ya samu karuwa
Mutumin da ya fi muni a Uganda ya samu karuwa

Mutumin nan da ya fi muni a kasar Uganda ya samu karuwar da namiji, inda yanzu ’ya’yansa suka kai takwas kamar yadda jaridar Metro ta ruwaito.

Mutumin mai suna, Godfrey Baguma, wanda aka yi amannar cewa yana fama da ciwon tabun hankali, ya ce ya yi farin ciki matuka da samun labarin haihuwar mai dakinsa.
Godfrey mai shekara 47 da haihuwa, ya karbi kambun wanda ya fi muni a kasar a shekarar 2002, bayan ya shiga gasar munin da fatan samun kudin da zai dauki nauyin iyalinsa da ke fama matsanancin talauci.
Mai dakinsa mai suna, Kate Namanda, ta ce tana jin dadin zama da mijinta. Godfrey yana da wasu ’ya’ya biyu da matarsa ta fari, wadda suka rabu bayan ya kama ta da laifin cin amanarsa.
Da aka tambaye shi yadda suka hadu da Kate, sai ya ce: “Sai da ta kwashe shekara hudu a gidana kafin iyayenta su fahimci cewa tana wurina. Ban bari sun san inda take ba, har sai bayan da muka samu haihuwa. Da ban yi hakan ba, da za a ba ta shawara ne ta rabu da ni,” inji shi.
Daga nan sai ya ce: “Ko da wannan dabarar, sai da ta bar ni lokacin da take da cikin wata shida, amma ina jin ta dauki dangana saboda ta dawo bayan wata biyu. Duk da haka na ba ta zabin cewa idan ta ga cewa ba za ta iya zama ba, tana iya tafiya. ”
Da aka tambayi Kate game da zamantakewarta da shi, sai ta ce: “Muna samun fahimtar juna tsakaninmu sosai. Abin da mutane ba su fahimta ba shi ne da zarar ka samu mutumin da kai a ganinka shi ne daidai da kai, to sai ka toshe kunnenka daga duk abin da jama’a za su fadi ”
Mista Godfrey ya auri Kate ne a shekarar 2013. Kuma a halin yanzu ’ya’yansu shida bayan haihuwarsu ta farko a shekarar 2008.

NAJERIYA A YAU: Turka-Turkar Da Ta Dabaibaye Zaben Jihar Edo

Ambaliya ta shafi mutum miliyan 1.6 a Nijeriya — NEMA

Haɗurra 3 sun yi ajalin mutane 91 a kwanaki takwas — FRSC

Abba zai gina wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa gidaje a Kano