Mutumin da ya hana aukuwar Yakin Duniya na Uku ya rasu
Tsohon jami’in sojin tsohuwar Tarayyar Sobiyet da ya hana barkewar Yakin Duniya na Uku, Stanislab Petrob ya rasu yana da shekara 77. Marigayi Stanislab Petrob ya rasu ne a a ranar 19 ga Mayu a garin Fryazino, da ke wajen Mosko, inda yake rayuwa shi kadai a kan kudin fansho, amma sai a ranar Litinin […]
Tsohon jami’in sojin tsohuwar Tarayyar Sobiyet da ya hana barkewar Yakin Duniya na Uku, Stanislab Petrob ya rasu yana da shekara 77.
Marigayi Stanislab Petrob ya rasu ne a a ranar 19 ga Mayu a garin Fryazino, da ke wajen Mosko, inda yake rayuwa shi kadai a kan kudin fansho, amma sai a ranar Litinin da ta gabata aka bayyana rasuwar tasa.
An bayyana cewa shi ne ya hana aukuwar yaki da makamin Nukliya a tsakani Tarayyar Sobiyet da Amurka, sakamakon wani tunani cikin gaggawa da ya yi a lokacin Yakin Cacar Baki.
Marigayin yana gudanar da aiki ne a wata cibiyar sirri ta soji da ke wajen birnin Mosko a ranar 26 ga Satumban 1983, lokacin da kwamfutocin Rasha suka yi kuskuren gano wasu makaman Nukiliya da aka harbo daga Amurka.
Wata fuskar kwamfuta ta nuna cewa an harbo wasu manyan makaman Nukiliya zuwa Rasha, kuma maimakon Petrob ya bi umarnin rundunar Red Army na sojin Rasha don daukar fansa, sai ya yi watsi da gargadin inda ya bugi kirjin cewa yana da ‘tabbacin’ cewa sanarwa ba gaskiya ba ce.
Petrob mai mukamin Laftana Kanar kuma yake da shekara 44 a lokacin, bai kai rahoton lamarin ga manyansa ba, kuma ba a samu bayanan yadda ya kwantar da hankalinsa ba a lokacin da yake cikin matsin sai bayan shekaru.
A wata tattaunawa da BBC a shekarar 2013, Petrob ya ce: “Jiniya ta yi kara, amma sai na zauna na tsawon wasu dakikai ina kallon babbar fuskar na’urar da aka rubuta kalmar ‘kaddamarwa’ a kanta. Abin da kawai na yi, shi ne in isa ga tarho; don shirya layin kaiwa ga manyan kwamandoji kai-tsaye – amma ban iya motsawa ba. Na ji kamar ina zaune a kan karfe mai zafi.” Kuma maimakon hanzarta kiran sojojin Sobiyet kamar yadda aka horar da shi, sai ya kira jami’in da yake bakin aiki a hedkwatar sojin ya ba shi rahoton cewa na’ura ta samu matsala.
“Bayan minti 33, sai na fahimci cewa babu abin da ya faru. In da an kawo hari, a lokacin zan sani. Sai hankalina ya kwanta,” inji shi.
Daga baya an gano kuskuren tauraron dan Adam ne ya haifar da sanarwar karyar, inda ya nuna bayyanar tartsatsin rana a saman gajimare da harin makaman Nukiliya. Tarayya Sobiyet ba ta karrama Petrob kan kyakkyawan tunaninsa ba, maimakon haka sai aka hana shi bayar da bayanin lamarin yadda ya kamata a cikin littafin bayanan aikinsa. Kuma ba a san abin da ya yi ba, sai a 1988, lokacin da aka ambace su a littafin tarihin kwamandan tsaron makaman Nukiliya na Sobiyet, Yury botintseb.
A shekarar 2006 ne wata kungiya mai suna Association of World Citizens ta karrama Petrob a hedkwatar Majalisar dinkin Duniya a matsayin ‘Mutumin da ya dakile yakin Nukiliya.’ Kuma an yi wani fim din tarihi a shekarar 2014 da aka sanya masa sunan Mutumin da Ya ceto Duniya.
Ba a bayyana dalilin rasuwarsa ba, kuma ya rasu ya bar ’ya’ya biyu mace da namiji.