Mutumin da ya ja jirgin kasa ya kashe wani yaro ya shiga hannu

Wani mutum mai shekara 41 zai gurfana a kotu bisa zargin ingiza wani yaro dan shekara 8 karkashin jirgin kasa da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Habte Araya, dan asalin kasar Eritiriya, mai fama da tabin hankali, ya tura yaron ne tare da mahaifiyarsa karkashin jirgin a shekarar 2018 a babbar tashar jirgin kasa ta Frankfurt […]

Mutumin da ya ja jirgin kasa ya kashe wani yaro ya shiga hannu

Wani mutum mai shekara 41 zai gurfana a kotu bisa zargin ingiza wani yaro dan shekara 8 karkashin jirgin kasa da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Habte Araya, dan asalin kasar Eritiriya, mai fama da tabin hankali, ya tura yaron ne tare da mahaifiyarsa karkashin jirgin a shekarar 2018 a babbar tashar jirgin kasa ta Frankfurt a kasar Jamus.

An ce mahaifiyar yaron da Allah Ya sa tana da tsawon kwana sai ta mirgine, jirgin bai bi ta kanta ba.

Mai gabatar da kara ya ce, ba duk abin da zuciyar Mista Araya ta saka masa yake da ikon kin aikatawa ba; amma, za a iya kama shi da laifin aikata kisan kai.

Haka nan kuma za a iya kara wa hukunci tsanani idan aka gano cewar Mista Araya “Ya nuna fin karfi ne ga wadanda abun ya faru da su”.

A yanzu dai ana zargin mutumin, mai ‘yaya uku da kokarin yin kisa. Haka nan kuma mai gabayar da karar ya nemi a kai shi a gidan masu hankali.

An kuma zargi Araya da kokarin tura wata tsohuwa yar shekara 78 gaban jirgin kasa, amma ta tsallake rijiya da baya-baya.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato