Mutumin da ya kashe matarsa ya shiga hannu
Wani mutum mai suna Shina Kasali mai kimanin shekara 38 ya fada hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan da ya yi ta jibgar matarsa mai suna Sofiyyat Kasali har ta rasu. Kakakin ’Yan sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa makwabtan ma’auratan ne suka ankarar da ’yan sandan abin da ya […]
Wani mutum mai suna Shina Kasali mai kimanin shekara 38 ya fada hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan da ya yi ta jibgar matarsa mai suna Sofiyyat Kasali har ta rasu.
Kakakin ’Yan sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa makwabtan ma’auratan ne suka ankarar da ’yan sandan abin da ya faru a Unguwar Abgado da ke Karamar Hukumar Ifo a ranar 1 ga Disamban nan.
Ya ce binciken da rundunar ta yi, wanda ake zargin wanda mahauci ne, ya ce a ’yan kwanakin nan lamari ya sukurkuce masa inda ya daina sana’ar fawar yake zaune ba ya komai, abin da ya sanya matar tasa ke yi masa kallon hadarin kaji tana raina shi.
Ya ce a ranar da lamarin zai faru yana zaune a kofar gida sai matar tasa ta zo wajen da yake ta yi masa kazafin cewa ya zauna ne yana kallon al’aurar wata karuwa take zaune a daura da shi, lamarin da ya fusata shi har ya kai ga rikicin nasu. Matar ta cika ne a lokacin da ake yunkurin kai ta asibiti, bayan dukan da mijin ya yi mata.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin tasa keyar wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka kafin daga bisani a gurfanar da shi a gaban kotu.