Mutumin da ya kashe uwarsa ya konata bisa zargin maita ya shiga hannu

Jami’an ’yan sanda sun nuna mai laifin, inda ya yi ikrarin aikata laifin da ake tuhumarsa da shi. Ekene, wanda baduku ne, ya ce ya zargi mahaifiyarsa da maita, hart a kai ga cewa yana ganin tana amfani da karfin maitarta wajen dakile ci gaban iyalansu, don haka ya yanke shawarar kasheta.Ya ce mahaifiyarsu ta […]

Mutumin da ya kashe uwarsa ya konata bisa zargin maita ya shiga hannu
Mutumin da ya kashe uwarsa ya konata bisa zargin maita ya shiga hannu

Jami’an ’yan sanda sun nuna mai laifin, inda ya yi ikrarin aikata laifin da ake tuhumarsa da shi. Ekene, wanda baduku ne, ya ce ya zargi mahaifiyarsa da maita, hart a kai ga cewa yana ganin tana amfani da karfin maitarta wajen dakile ci gaban iyalansu, don haka ya yanke shawarar kasheta.
Ya ce mahaifiyarsu ta yi amfani da maitarta a kan ’ya’yanta hudu, domin har yanzu wansa dan shekara 45 bai yi aure ba, kuma babu wanda ya yi aure a cikin zuri’arsa.
“Mahaifiyarsa ta hana ruhin Ubangiji shiga cikin zuriarmu, kuma duk wanda tat sine mawa ba zai taba ci gaba ba,” inji shi.
Da yake bayani kan yadda ya kasheta, ya ce a wannan ranar, ya soketa da wata sanda da daddare, sai kawai ta fadi ta mutu. Sai ya dauki gawarta a cikin karamar kura (baro) zuwa dajin Obukwu, inda ya konata ta zama toka.
Ya ce ya gudu zuwa Jihar Abiya, inda rundunar ’yan sanda ta musamman (SARS) ta kama shi. Duk da cewa ya yi nadamar kashe mahaifiyarsa, yace inda mulkin Ubangiji ya tabbata, mutane za su gane cewa ya aikata abin da ya dace.
Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sanda (PPRO), Mista Uche Eze, wanda ya nuna wa manema labarai wanda ake zargi da aikata laifin, ya ce ana ci gaba da bincike.

Barau ya buƙaci Ganduje ya ƙwato wa APC ƙarin jihohi

An kama masu laifi 30,000 a 2024 – Sufeto Janar na ’Yan Sanda

DAGA LARABA: Dalilan wasu darikun Kirista ba sa bikin Kirsimeti

PCAACC ta karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano