Mutumin da ya ‘rasu’ a hatsarin jirgin sama ya dawo gida bayan shekara 45

Twason shekarun dai an yi zaton ya rasu a hatsarin jirgin.

Mutumin da ya ‘rasu’ a hatsarin jirgin sama ya dawo gida bayan shekara 45

Sajjad Thangal kenan tare da mahaifiyarsa

Mahaifiyar wani mai shekara 70 mai suna Sajjad Thangal wadda a yanzu take da shekara 91 da ’yan uwa suna can suna ta mamaki a kasar Indiya, inda danta ya dawo bayan shekara 45 da tunanin ya rasu a wani hatsarin jirgin sama.

Abin mamakin ya faru ne a kauyen Ashram da yake yankin Panvel a wajen birnin Mumbai a wannan mako bayan da mutumin da aka dauka ya rasu a hatsarin jirgin saman ya dawo cikin danginsa.

Abin farin cikin ya auku ne a wata cibiya ta Kungiyar Soyayya da Bushara mai suna Social and Evangelical Association for Love (SEAL) da ke Ashram, lokacin da iyalan mutumin suka isa can bayan sun samu labarinsa domin tafiya da shi gida.

Iyalan da dan uwan nasu da ya bace, sun isa garin Kollam a gundumarsu da take Kudancin Kerala a ranar Asabar da ta gabata.

Kuma mutanen da suka halarci bikin maraba da shi sun haura 100, ciki har da danginsa daga masu shekara biyu zuwa mahaifiyarsa mai shekara 91.

Mutanen kauyen sun shirya bikin ‘tarbarsa’ a gidansu inda aka yanka kek don murnar wannan rana kuma dan majalisar yankin Kovoor Kunjumon ya halarci bikin.

Sajjad Thangal dai yana matashi dan shekara 25 aka yi zaton ya rasu tare da mutum 94 a wani hatsarin jirgin saman Indian Airlines wanda ya tashi daga Mumbai zuwa Madras kuma ya yi hatsari a ranar 12 ga Oktoban 1976.

Thangal yana dillancin fina-finai ne a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a shekarun 1970, kuma ya taba shirya bikin rawa na Rani Chandra, daya daga cikin fitattun jaruman Malayalam da tauraronsu yake haskakawa a shekarun 1970.

An tsara Thangal zai yi rakiya ga jarumar da ayarinta zuwa Kerala, amma sai wasu hidimomi suka hana shi shiga jirgin da ya yi hatsarin.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa