Mutumin da ya sanya wanduna takwas da riguna 10 ya shiga hannu

An kama wani mutum a babban filin jirgin saman Iceland Keflabík saboda sanya tufafi masu yawa. Ryan carneey Williams, wanda aka fi sani da Ryan Hawaii a shafukan sada zumuntar intanet, ya taso daga kasar Iceland zuwa England a jirgin British Airways. Yana sanye da kamfai da wanduna takwas da riguna 10, wato kayayyakin da […]

Mutumin da ya sanya wanduna takwas da riguna 10 ya shiga hannu

An kama wani mutum a babban filin jirgin saman Iceland Keflabík saboda sanya tufafi masu yawa. Ryan carneey Williams, wanda aka fi sani da Ryan Hawaii a shafukan sada zumuntar intanet, ya taso daga kasar Iceland zuwa England a jirgin British Airways. Yana sanye da kamfai da wanduna takwas da riguna 10, wato kayayyakin da suka ki shiga jakarsa, inda ya yi hakan don kauce wa biyan karin kudin dakon nauyin kaya.

An hana shi hawa jirgin saboda dimbin kayan da ke sanye a jikinsa bayan da jami’an tsaro suka duba shi.

A hoton bidiyon da aka baza a shafin twitter, ma’aikatan jirgin saman sun yi tuntuba kan ko akwai bukatar a kirawo ’yan sanda.

Shi kuwa a sakonsa na twitter cewa ya yi @British_Airways sannu an tsare ne a filin jirgin saman Iceland Keflabik saboda ba ni da jaka sai na sanya daukacin kayana, duk da haka suna hana ni tafiya. Ko wariya ce (ake nuna mini)?

Ya yi ta surutai wai a kan cewa shi an nuna masa wariya.