Mutumin da ya shafe shekara 60 ba wanka ya mutu

Amou Haji ba da jimawa ba bayan an tilasta mishi wanka, wanda shekara 60 rabonsa da yi

Mutumin da ya shafe shekara 60 ba wanka ya mutu

Rahotanni daga Iran sun tabbatar da mutuwar Amou Haji da aka ce shi ne uban masu dauda na duniya.

Kafar yada labaran yankin ta ce, a ranar Lahadi Haji ya rasu a kauyen Dezhgah, inda ya bar duniya yana da shekara 94.

Kafar ta ce, a halin rayuwarsa marigayin ya shafe shekara 60 ba tare da wanka ba, wanda ake zargin hakan ya yi silar rashin lafiyar da ya yi fama da shi.

An ce a tsakanin ’yan watannin da suka gabata mazauna kauyen suka matsa a kan sai marigayin ya yi wanka, inda suka dauke shi zuwa makewayi suka yi masa wanka, kamar yadda jaridar Telegraph ta rawaito.

Jaridar ta kara da cewa, bayan yi masa wanka ba da dadewa ba ya soma rashin lafiya wanda a Lahadin da ta gaba ta ya ce ga garinku nan.

Bayan rasuwar Haji, ana kyautata zaton wani dan kasar Indiya mai suna Kailash “Kalau” ne ya zama magajin Amou Haji, wanda aka ce rabonsa da wanka tun a 2009.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan