Mutumin da ya shuka itatuwan kuka 3,000 cikin shekara 47
Dasawa ko shuka itatuwan kuka a yanzu wani bangare ne na imanin El Hadji.
Wani dattijo mai suna El Hadji Salifou Ouédraogo ya shafe shekara 47 yana shuka itatuwan kuka sama da 3,000 a garinsu na Titao, a kasar Burkina Faso.
Mutane da dama sun san amfanin itaciyar kuka, ba kawai don ana amfani da ganyenta wajen yin garin kuka da ake yin miya a ci tuwo da ita ba, tana kuma magani.
Kuma akwai abubuwa da yawa da ake yi da wasu sassanta, mafi muhimmanci kuma shi ne kyautata muhalli, yaki da zaizayar kasa da magance wa dumamar yanayi.
Itaciyar kuka ana kiranta baobab da Ingilishi kuma tana rayuwa mai ban sha’awa a cikin yankunan sabannah, tana ba da tsarin yin muhalli da abinci da ruwa ga mutane da nau’o’i tsirrai daban-daban.
Hakan ya sa a cikin shekara 47 da suka gabata, El Hadji Salifou Ouédraogo ya samar da wani katafariyar gona da ke taimaka wa danginsa, da al’ummarsa da kuma duniya ta hanyar shuka itatuwan kuka.
An haifi El Hadji kuma ya girma a garin Titao, a kasar Burkina Faso, ya yi marmarin zama makarancin Alkur’ani.
Ana yi masa da lakabi da mai sha’awar tsirrai, zuwa wani lokacin saboda yanayi.
Da farko, El Hadji ya fara da dasa itatuwan mangwaro amma ya gane cewa duk wanda ke kusa da shi yana yin haka.
Sha’awar zama daban ya sa ya fara shuka kukoki da yawa. Mutane suna kiransa mahaukaci, amma hakan ya kara karfafa wa El Hadji gwiwa.
A cikin al’adun gargajiya na yankinsa, duk wanda ya shuka kuka ta mutu, to zai fuskanci wasu matsaloli.
Bayani ya nuna cewa itaciyar kuka na alfahari da wanda ya shuka ta, don haka wasu suka dauke ta abar bautarsu suna fushi da masu sare itatuwan kuka da fushi ga masu tumbuke su.
El Hadji ya gaya wa jama’ar yankin cewa, “Mahaifina bai shuka kuka ba, amma ya rasu.
“Ban taba ganin kukar da mahaifina ko kakana ya shuka ba, amma duk sun rasu. Idan itaciyar kuka ta rayu kuma na rasu, ba matsala ba ce.
“Duk da wannan tatsuniya, itaciyar kuka na da muhimmanci ga rayuwa a cikin sabannah.
“Itaciyar mai dandano, ana shan ta kuma tana adana ruwa daga lokacin damina a cikin babban jikinta, wanda ke taimaka wa yanayin kasa ya zama da danko, kuma tana rage zaizayewar kasa, kuma ta zama tushen ruwa ga dabbobi da yawa.
’Ya’yan itaciyar kuka sun ƙunshi sunadarin tartaric acid da Bitamin C, suna samar da muhimman abubuwan gina jiki ga nau’o’in halittu, ciki har da tsuntsaye, kadangaru, birai, har ma da giwaye.
Ga mutane, ana iya cin ’ya’yan itacen kuka, a jika a cikin ruwa don yin abin sha mai dadi, a adana shi a cikin gora, ko a busar da su kuma a nika don yin sinadarin kofi.
A yau, gonar kukoki ta El Hadji tana da itatuwan kuka sama da 3,000 kuma tana da fadin hekta 14.
Kukokin ba kawai suna samar da abinci ga mutanen kauyensa ba ne, har ma suna kiyaye rayuwar al’adu tare da kare yanayin daga illar sare dazuzzuka.
Dasawa ko shuka itatuwan kuka a yanzu wani bangare ne na imanin El Hadji.