Mutumin da ya yanke gabansa yana tsaka da mafarkin yanka nama
Ya ce bai ma san ya yanke ba, sai da aka kai shi asibiti
Wani mutum mai suna Kofi Atta dan kasar Ghana, ya yanke gabansa yana tsaka da bacci, in da ya ce mafarki ya yi yana yanka nama don yi wa ‘yan gidansu girki.
A zantawarsa da BBC, Kofi ya ce ko bayan yanke gaban nasa bai farka daga baccin ba, har sai da aka kai shi asibiti don yi masa tiyata.
- Za a sami ambaliyar ruwa a Sakkwato, Kebbi da Borno kwanan nan – NiMet
- LABARAN AMINIYA: Nan Ba Da Jimawa Ba Zan Bayyana Matsayina Kan Batun Ficewa Daga NNPP – Shekarau
“Bacci ya dauke ni da rana ina zaune kan kujera, kuma ban san ma ya aka yi na dauko wukar ba.
“kawai dai na san na yi mafarki ina yanka nama ina mikawa dangina, ashe gabana nake yankewa.
“Zafin yankan bai sa na tashi daga baccin ba, sai ihu da nake a mafarki, duk jini ya wanke ni, sanda na farka har makwabta sun kai ni asibiti,” inji shi.
Mutumin dai, wanda manomi ne mai shekara 47, mazaunin garin Assim Akomfode ne da ke kasar ta Ghana.
Likitocin da suke kula da shi sun ce da zarar an kammala yi masa tiyata, zai koma daidai.