Mutumin da ya yi shekara biyar yana shan fitsarinsa a birnin Landan
A wani lamari mai kama da almara a birnin Landan, wani mutum mai suna Dabe Murphy ya kwashe sama da shekara biyar yana shan fitsarinsa kuma yana wanka da shi. Dabe mai shekara 54 ya ce shan fitsarin nasa wanda ake ganin kamar shirme yake yi, yana taimaka masa wajen magance ciwon asama (asthma) sannan […]
A wani lamari mai kama da almara a birnin Landan, wani mutum mai suna Dabe Murphy ya kwashe sama da shekara biyar yana shan fitsarinsa kuma yana wanka da shi.
Dabe mai shekara 54 ya ce shan fitsarin nasa wanda ake ganin kamar shirme yake yi, yana taimaka masa wajen magance ciwon asama (asthma) sannan kuma ya taimaka masa wajen samun jiki mai kyau kamar bai tsufa ba.
Dabe Murphy ya kwashe kimanin shekara shida yana yin wanka da fitsarinsa, sannan kuma bayan shekara daya da fara yin wankan, sai ya fara shan fitsarin.
Shi dai Dabe dan garin Basildon ne da ke yankin Essed na birnin Landan.
A kullum, abincin Dabe Murphy bai wuce cin ’ya’yan itace ba, sannan ya kora kofi biyu na fitsarinsa. Kuma a shekara ta 2012, Dabe Murphy ya taba kwashe kwana 30 ba abin da ya saka a bakinsa sai fitsarinsa kawai.