Mutumin da ya yi ta lalata da ‘yar cikinsa ya shiga hannu
Dubun wani mutum mai shekaru 41 mai suna Sikiru Odedeji ta cika bayan da ya yi ta lalata da ’yar cikinsa mai kimanin shekaru 13 tun bayan rabuwarsa da matarsa da ta haifa masa ’yar. A cewar kakakin rundunar Jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi mahaifiyar yarinyar ce ta shigar da kara a ofishin rundunar da […]
Dubun wani mutum mai shekaru 41 mai suna Sikiru Odedeji ta cika bayan da ya yi ta lalata da ’yar cikinsa mai kimanin shekaru 13 tun bayan rabuwarsa da matarsa da ta haifa masa ’yar.
A cewar kakakin rundunar Jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi mahaifiyar yarinyar ce ta shigar da kara a ofishin rundunar da ke garin Sango Ota, inda ya ce ’yarinyar wacce aka sakaya sunanta ne ta fallasa muguwar daibi’ar mahaifinta, inda ta sanar wa mahaifiyarta da ke zaune a Legas halin da take ciki. Ta ce tun bayan rabuwarsu ne mahaifinta ke yin lalata da ita tun a karshen shekarar 2016. A cewarta yawan lalatar da yake yi da ita ne ya sanya ta kasa jurewa ta sanar da mahifiyarta duk da barazanar da ya yi mata na cewa muddin ta sake ta fada zai kasheta.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya alakanta hakan da aikin shaidan. Tuni dai rundunar ’yan sandan karkashin umarnin kwamishinan ’yan sandan Jihar Ahmad Iliyasu ta tasa keyarsa zuwa sashen kare hakkin yara na rundunar, domin zurfafa bincike kafin daga bisani a gabatar da shi a gaban kuliya.