Mutumin Denmark ya kera wa tsuntsaye shekar zamani a birane

Thomas Dambo, wani gwanin zayyana, ya shafe shekara bakwai yana kera wa tsuntsaye wasu kananan gidaje ko “shekar zamani da ya kan sagale a bishiyoyin birane da ke fadin duniya.daukacin wadannan shekaru Dambo yana amfani da guntattakin katakaye da aka zubar, inda ya kera wadannan nau’ukan sheka ta zamani ko gidan tsuntsaye” har dubu uku […]

Mutumin Denmark ya kera wa tsuntsaye shekar zamani a birane
Mutumin Denmark ya kera wa tsuntsaye shekar zamani a birane

Thomas Dambo, wani gwanin zayyana, ya shafe shekara bakwai yana kera wa tsuntsaye wasu kananan gidaje ko “shekar zamani da ya kan sagale a bishiyoyin birane da ke fadin duniya.
daukacin wadannan shekaru Dambo yana amfani da guntattakin katakaye da aka zubar, inda ya kera wadannan nau’ukan sheka ta zamani ko gidan tsuntsaye” har dubu uku da 500. Sai dai duk da wadannan gidaje day a kera wa tsuntsaye, ba yana nufin kai tsaye tsuntsaye za su shige ciki ba ne.
Dambo dayana da tabbacin cewa sagale shekar zamani a wurin da ya dace shi ne muhimmin al’amari. Don haka yake ganin in har aka rataye irin wannan gidan tsuntsu a farin turke mai tsawo a titi mai hada-hada da hatsaniya, tsuntsaye ba za su shiga ba.
Ko me ya jawo hankalin sa wajen kera irin wadannan gidajen tsuntsaye? Sai ya ce kera shekar zamani ba yana nufi bai wa tsuntsu kariya ce ba kawai, a’a, al’amarin nma tuni ga mutane kan lallai su tanadi matsugunni ga sauran halittu.