Mutumin kirki ya dace a zaba ba jam’iyya ba – Shugaban NDP
Shugaban Jam’iyyar NDP reshen Jihar Bauchi, Malam Abubakar dandada ya ce lokaci ya yi da ya kamata mutane su zabi mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana domin yanzu siyasar Najeriya ta canza mutum ya kamata a yi ba jam’iyya ba. Malam Abubakar dandada bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa […]
Shugaban Jam’iyyar NDP reshen Jihar Bauchi, Malam Abubakar dandada ya ce lokaci ya yi da ya kamata mutane su zabi mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana domin yanzu siyasar Najeriya ta canza mutum ya kamata a yi ba jam’iyya ba.
Malam Abubakar dandada bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi, inda ya yi kira ga al’ummar Jihar Bauchi su daina siyasar jam’iyya su zabi mutumin kirki a zaben Sanata da ’yan majalisar wakilai da na dattawa.
Har ila yau ya bukaci al’ummar jihar su zabi Gwamna Isa Yuguda a matsayin Sanata daga mazabar Bauchi ta Kudu saboda a cewarsa ya cancanata.
Daga ya yi kira ga dillalan ’yan siyasa su rika taka-tsantsan game da abubuwan da suke fada a lokacin da suke tallata ’yan takararsu a kafafen watsa labarai.