Mutumin Sin ya kewaya birane 40 da matarsa mai shanyayyen jiki a mota mai taya uku

Wani mutumin kasar Sin ya mayar da babur dins amai taya uku motar tafi-da-gidanka, inda ya dauki matarsa mai shanyayyen jiki ya kewaya da ita biranen kasarsu 40 cikin shekara bakwai. Matar Guo Jingdin ta fama da ciwon zubar da jinni a kwakwalwa shekara bakwai, inda ta shafe shekara da wata a some bayann da […]

Mutumin Sin ya kewaya birane 40 da matarsa mai shanyayyen jiki a mota mai taya uku

Wani mutumin kasar Sin ya mayar da babur dins amai taya uku motar tafi-da-gidanka, inda ya dauki matarsa mai shanyayyen jiki ya kewaya da ita biranen kasarsu 40 cikin shekara bakwai.

Matar Guo Jingdin ta fama da ciwon zubar da jinni a kwakwalwa shekara bakwai, inda ta shafe shekara da wata a some bayann da aka yi mata aiki. Bayan da ta farfado daga suma, Guo ya yi tunanin kewaya kasar da ita, don  haka ya mayar da babur dinsa mai taya uku ya zama motar tafi-da-gidanka.

Kullum Guo yana yi wa matarsa tausa ya ja-mata gabob in jiki don kada su daddaure su langabe.

Muna tafiya a motar ban sha’awa, mu ci abincin da ya ba mu sha’awa, amma rayuwarmu mai sauki ce, inji Guo.

Wadanan ma’aurata da suka fito daga Lardin Henan sun kewaya birane 40 na kasar Sin, wadanda suka hada da di’an da Beijing, har ma da wuraren da suka hada da Henan.

Za a rataye mutane 3 kan kisan kwamandan soji

DAGA LARABA: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2