Mutunci Sardauna ya bar wa iyalansa ba dukiya ba – Farfesa Mukhtar
Farfesa Mukhtar Umar Bunza na sashen Tarihi a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, ya ce a fahimtar da ya yi, Sardauna Ahmadu Bello mutum ne haziki, ‘Dukkan rayuwarsa za ka ga yana da hangen nesa da yin tsari wanda yake ba na son kai ba, don dai al’umma ta ci gaba, duk inda yake […]

Farfesa Mukhtar Umar Bunza na sashen Tarihi a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, ya ce a fahimtar da ya yi, Sardauna Ahmadu Bello mutum ne haziki, ‘Dukkan rayuwarsa za ka ga yana da hangen nesa da yin tsari wanda yake ba na son kai ba, don dai al’umma ta ci gaba, duk inda yake haka ne, tun daga zamansa a Gusau da Rab,ah har Allah Ya sanya ya shiga siyasa, inda ya gina al’umma ba da yaudara ko cutarwa ba. Muradinsa ya cika, ya raya jama’arsa da ilmi a kowane fanni, da da samar da sana’ar da ake iya dogaro da ita da samar da masana’antu don bunkasa harkar noma da kasuwanci a Arewa.
Ya kara dacewa,’’ Sardauna ya samar da ruwa a gefen Barno cikin hamada kuma har yanzu suna amfani da shi, a lokacin yana sanyawa ne a tono ruwa a bar shi yana gudana a daji, mafi yawan damshin da jihar take da shi aikin nan ne da ya aiwatar. Duk abin da zai sanya a yi wannan al’ummarsa dariya sai da Sardauna ya yi kokarin kauce masa. Dubi kamfanin siminti na Sakkwato da Bankin Arewa da kamfanoni da masana’antu da sauransu. Sardauna ya yi wa jama’a hidima ne bai yi wa kansa komai ba. A Sakkwato ko gida bai gina ba. Akwai wani kundi da na karanta, Firimiya yana kan mulki sai da ya ci bashin gwamnati na Fam dubu biyu, takarda ya rubuta a rubuce yana neman rance ya cika ya sayi mota, bayan ya samu a alawus na tafiye-tafiyen da ya yi ya biya kudin, kundin yana nan a ajiye a gidansa na Kaduna. Wannan shi ne fa a lokacinsa yake sanya hannu a bai wa gwamnatin Ingila bashin kudi, ya yi kokari sosai ya raya mutanen baya, ya rage na bayan su dauka ko su ajiye, sai dai kash! Mafi yawan mutanen ba su dauka ba, domin a bayansa abin da aka dauka samar da cigaba shi ne sace kudin kasa a tara wa ‘ya’ya da jikoki, ita ce matsalar da muke fama da ita.’’
Farfesa Mukhtar ya cigaba da cewa, ‘’Shi dai Sardauna bukatarsa ta biya, ya gina Arewa, ya rage Arewa ta gina kanta ko ta rushe kanta, kamar yadda ta yi yanzu, don yadda mutanen Arewa suke yanzu ba haka Sardauna ya so su kasance ba, mafi yawan shugabaninmu son kansu ya fi son al’ummarsu, wanda hakan ya samar mana duk wani wulakanci, mu ne bara da roko da bambandanci da mutuwar zuci da jahilci, abubuwan da su Sardauna ba su gina tubalinmu kan haka ba. Dama shi tarihi amfaninsa sanin baya, idan ka yi da kyau ka sani, idan ka yi akasin haka ma ka sani, don ka gyara ko ka kara kaimin abin da kake aiwatarwa. Sardauna Shakara 50 ba a manta da alherinsa ba, ana tunawa da shi. Da dukiya ce ya bari da yanzu ta kare kuma iyalansa sun bace bat, amma ka ga yanzu mutuncin da ya bar musu ya fi dukiyar da aka bar wa wadansu. Al’umma su yi tunani, kudi ba su ba ne, mutunci da tsaron gaskiya da amana da yi wa al’umma aiki shi ne abin tinkaho gare ,ka da danginka don ka ga Sardauna har yanzu shi kadai ake ambato.’’