Mutunta addinai: Buhari ya koya mana darasi mai kyau – Namadi

Mataimakin Shugaban kasa Muhammed Namadi Sambo ya ce ganawar da dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya yi da shugabannin addinin Kirista daga yankin Arewa maso Gabas wata hanya ce a bar misali na samar da zaman lafiya da lumana da kuma mutunta juna a tsakanin mabiya addinai. Alhaji Mohammed […]

Mutunta addinai: Buhari ya koya mana darasi mai kyau – Namadi
Mutunta addinai: Buhari ya koya mana darasi mai kyau – Namadi

Mataimakin Shugaban kasa Muhammed Namadi Sambo ya ce ganawar da dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya yi da shugabannin addinin Kirista daga yankin Arewa maso Gabas wata hanya ce a bar misali na samar da zaman lafiya da lumana da kuma mutunta juna a tsakanin mabiya addinai.

Alhaji Mohammed Namadi Sambo ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron fadakarwa da wayar da kan malaman Musulunci kan gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba da aka yi a Kaduna a ranar Lahadi.
Namadi Sambo ya ce ganawar ta Buhari wata manuniya ce cewa ’yan Najeriya za su iya zama tare ba tare da lura da bambancin addini ko kabila ba, ya ce da Allah Ya so da ya mayar da daukacin ’yan Najeriya Musulmi ko Kirista.
“Lokacin da dan takarar Shugaban kasa na APC ya ziyarci shugabannin addinin Kirista daga Arewa maso Gabas ya nuna wa daukacin ’yan Najeriya wajibi ne mu zauna lafiya da juna. Sun ma ba shi kyautar littafin Baibul kuma ya karba, bai ce shi Musulmi ba ne ko ya ki halartar wannan ganawa,” inji Namadi.
Ya kara da cewa, “Wannan babban abin alheri ne, kuma Janar Buhari ya yi abin misali don amfanin kasarmu. Ya kamata a bambanta addini da siyasa, kuma wannan ne abin da gwamnatin Goodluck Jonathan take ta kira a kai tun hawanta karagar mulki.”
Ya ce tunda aka samun ’yanci Musulmi da Kirista ke aiki tare, kuma wannan ya nuna Allah ne kawai zai iya mayar da daukacin wata al’umma mai bin wani addini idan Ya so, kuma babu mai iya tuhumar haka.
Mataimakin Shugaban kasar, ya kuma yi kira ga malaman da su ilimantar da mabiya a kan bin Allah da kuma girmama shugabanninsu. “Akwai bukatar malamai masu wa’azi su shawarci masu zabe a kan bukata da muhimmancin zaman lafiya kafin da lokaci da kuma bayan zabe,” inji shi.
A jawabin Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ce malamai na da gudunmawar bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin gudanar da zabe.
Wanda ya shugabanci taron kuma mai bai wa Shugaban kasa Shawara a kan Addinin Musulunci da kula da Masallacin Fadar Shugaban kasa, Barista Tahir Umar Tahir ya ce an shirya taron ne ga malaman yankin saboda su taimaka wajen tabbatar da an yi zabe ba tare da rikici ba tare kuma da hada kan al’ummar kasa.