…Mutuwa domin wani asara ce

Idan aka yi zabe na gaskiya da wuya a tada hankali -Sheikh Tureta Sheikh Abubakar Tureta wani sanannen malami ne da ke zaune a Kaduna, ya zanta da Aminiya a kan zabe mai zuwa inda ya shawarci matasa da su kauce wa bangar siyasa, sannan su kuma ‘yan siyasa su daina yin amfani da matasa […]

…Mutuwa domin wani asara ce

Idan aka yi zabe na gaskiya da wuya a tada hankali -Sheikh Tureta

Sheikh Abubakar Tureta wani sanannen malami ne da ke zaune a Kaduna, ya zanta da Aminiya a kan zabe mai zuwa inda ya shawarci matasa da su kauce wa bangar siyasa, sannan su kuma ‘yan siyasa su daina yin amfani da matasa wajen ingiza su suna tada hankulan jama’a. Su kuma malamai ya gargade su su guji zama ‘yan barandan ‘yan siyasa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Daga gobe za a fara gudanar da zabe a kasar nan, wane jan hankali za ka yi wa al’umma domin ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali?
Shaikh: Da farko dai su shugabanni hakkinsu ne su tabbatar da an yi zabe cikin gaskiya. Idan aka yi gaskiya wajen zabe har talaka ya tabbatar da cewa abin da aka yi iyakar gaskiyar ke nan hankalinsa ba zai tashi ba. Amma idan aka yi ba daidai ba ko yake ganin ba a yi adalci ba, shi ke kawo hankali ya tashi har ya yi wani abu da shari’a ba ta yarda da shi ba. Saboda haka rikicin siyasa da ake yi mafi yawa shugabanni ke haddasa shi. Misali, zabubbukan da aka yi a kasar Amurka tun daga na Clinton har zuwa na Barak Obama duk mun ga yadda ake ta fadi tashi wajen kirgen kuri’a aka gama aka ce ba a yarda ba, har aka dawo a sake kirge da hannu. Amma har aka gama ran kowa bai baci ba. Kuma da aka tabbatar da wanda ya ci sai aka sanar. Shi wanda bai ci ba ya taya wanda ya ci murna. Toh, muna fatan a yi koyi da irin wannan tsari, tunda daga can aka koyo tsarin na Damokradiya.
Na biyu, har yau dai su ‘yan siyasa masu ingiza matasa su saya musu kayan shaye-shaye ko kuma su saya musu makamai irin su adda da takobi da sauransu, ‘yan sanda kuma na ganin ana wasa irin wadannan makamai bisa titi, ga kuma manyan ‘yan siyasa duk suna gani amma a ki daukar mataki, shi ma illa ne sosai. Kiran da nake yi shi ne, a yi kokari wadannan abubuwa biyu da na ambata a janye su. Idan aka yi hakan, shi talaka ya ga an yi gaskiya ga zabe, sannan ba a ba shi makami don ya tada hankali a lokacin zabe ba, ina ganin idan Allah Ya yarda aka yi zabe duk wanda ya ci aka ba shi, da wuya a samu tashin hankali.
Aminiya: Wane jan hankali za ka yi ga su ‘yan siyasa masu ingiza matasa suna tada rikici lokacin zabe?
Sheikh: Sune bangaren shugabanni wadanda na ce su janye wannan dabi’a din ta ingiza matasa. Ai idan ka ga yaro ya je ya zagi babba ai wani ya ingiza shi. Ai kowa ya san doka, idan har ka ga mutum ya zo ya duki wani a gaban manya, ai manyan suka sa shi. Amma idan ya san cewa idan ya yi rigima za a kama shi a kulle ba zai yi ba.
Suma yaran ana yaudararsu, domin babu dan dan siyasa cikin masu tada rigima, ko kanin matarsa ko wani na kusa da shi, sai ‘ya’yan talakawa kawai, su kashe a kashe su, wanda kuma asara ce babba ake yi tunda muna da bukatar wadannan talakawan. Muna kira ga irin wadannan ‘yan siyasa da su ji tsoron Allah su daina irin wadannan dabi’u domin ba shari’a ba ce, kuma shi kanshi tsarin damokaradiyyan bai yarda da hakan ba. Tsarin damokaradiyyan bai zo da tsarin kashe-kashe ba. Jahilci ne da rashin hangen nesa ke sa mutane kashe junansu saboda siyasa.
Aminiya: Ina matsayin matashin da ya rasa ransa wajen rikicin siyasa a musulunci?
Sheikh: Annabi ya ce idan musulmi biyu suka hadu da takubba suka yi fada da wanda ya kashe da wanda aka kashe duk ‘yan wuta ne. Aka tambaye shi cewa wanda aka kashe ma yana da laifi? sai ya ce shi ma ai da nufin kisan ya fito. Ashe niyyar da ya fito da ita domin kashe dan uwansa amma sai shi aka riga kashe shi ya isa shi ma ya zama dan wuta, don haka wanda ya taimaka aka kashe mutum ko da da rabin kalma ce Annabi ya ce sai ya dauwama a wuta.Saboda haka su matasa su sani cewa iyayensu sun haife su ne domin su yi masu amfani, ba su haife su domin su aikata abin da ba zai amfane su ba, har ta kai ga sun kashe kansu, bayan iyayensu sun gama wahala da su. Idan suka yi haka sun ci amanar iyayensu sun kuma ci amanar al’umma da suka rayu cikinta, domin al’umma na binsu bashi.
Aminiya: Wane kira za ka ga malamai domin su kauce wa karbar kyauta daga ‘yan siyasa?
Sheikh: Musulunci bai haramta wa malami yin siyasa ba, idan har malami na da sha’awar yin siyasa kuma yana da abin yin siyasa sai ya fito ya nemi mukamin siyasa, gwamna ko Sanata ko dan majalisar wakilai ko na jaha. Amma malami ya zama dan barandan dan siyasa a ba shi kudi ya tafi ya je ya yaudari mutane su zabi wani wanda ya san ba mutumin kirki ba ne, idan ya yi haka ya cuci addinin Allah ya kuma cuci al’umma. Na yi magana kwanakin baya inda na ce malamai akwai nauyin da Allah Ya dora musu wanda idan ka amshi kudin dan siyasa aka zabe shi ayyukan da bai yi ba wanda ya kamata ya yi ba ka iya yi masa magana ya yi su, domin ya rigaya ya saye ka ya biya. Ba ka da bakin yi masa magana domin yin aiki, domin ka rigaya ka sayar da kanka gare shi ya kuma biya ka. Amma idan ka tsaya bisa gaskiya, ko ya ba ka kudi ko kar ya ba ka,lokacin da aka yi zabe ya ci sai ka wasa takobinka na tunkararsa ga dukkan abin da ya shafi al’umma cewa lallai abin da al’umma ke so a tabbata an yi musu. Muna da bukatu da yawa, akwai musamman harkar tsaro da harkar lafiya da noma da ilimi da kyautata rayuwar jama’a da yin hanyoyi da sauransu.
So da yawa za ka ga an dauko mace a kan jaki kafin a kai asibiti ta mutu saboda nakuda, ga kuma rashin hanya. Malamai idan suka karbi kudi a hannun ‘yan siyasa ba su da ikon yi masu magana a gyara wadannan hanyoyi. Annabi ya ce, akwai wadansu mutane idan suka gyaru al’umma ta gyaru, idan kuma suka lalace al’umma ta lalace, sune malamai da masu mulki.
Masu mulki makafi ne, malamai su ke gani su sanya su a hanya, domin su suka san abin da ya kamata, su kuma suka san abin da ya dace a yi kuma su ke fadi a ji. Idan suka karbi kudi sai su zama makafi kurame, don haka ka ga ashe gwanda makaho da kurma kuma makaho. Don haka lallai ne malamai su daure su kauce wa karbar kudi na rashawa, domin da malami ya karbi kudi zuciyarsa sai ta mutu, idan ya ga ba daidai ba zai iya yin magana a kai ba. Sai a yi kokari a kauce wa wannan rami.
Aminiya: Ko akwai laifi idan malami ya nemi al’umma su zabi dan tankara a bisa cancantarsa ko da kuwa a wace jam’iyya yake?
Sheikh: Babu laifi malami ya nunawa almajirai ko mabiyansa ko masu binsa sallah cewa wane shi ya fi dacewa a zaba, babu laifi idan dai ba jinga aka yi da kai ba. Ba kuskure ba ne daidai ne a nuna wa mutane ga wanda ya dace kuma a fadi abubuwan da ya aikata.