Mutuwa mai rusa jin dadi (II)

Hudubar Imam Awwal Isa Umar, Masallacin Juma’a na Khalid Bin Walid, Awalah, Bauchi Huduba ta Farko:Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya halicci sammai ba tare da wasu turaku da kuke ganinsu ba. Godiya ta tabbata ga Allah, kuma Shi ne Ma’ishi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata bisa BawanSa da Ya zaba, Annabinmu […]

Mutuwa mai rusa jin dadi (II)
Mutuwa mai rusa jin dadi (II)

Hudubar Imam Awwal Isa Umar,

Masallacin Juma’a na Khalid Bin Walid, Awalah, Bauchi

Huduba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya halicci sammai ba tare da wasu turaku da kuke ganinsu ba. Godiya ta tabbata ga Allah, kuma Shi ne Ma’ishi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata bisa BawanSa da Ya zaba, Annabinmu Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da wanda ya jibince shi. Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya hukunta mutuwa a kan bayinSa, kuma Ya kadaita da rayuwa da tabbata.
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma sai magagin mutuwa ta zo da gaskiya.” Kuma Madaukaki Ya sake cewa: “Kowace rai mai dandanar mutuwa ce, kuma wallahi za Mu jarrabe ku da alheri da sharri a matsayin fitina, kuma gare Mu ake mayar da ku.”
Bayan haka, ku tsoron Allah ya ku Musulmi matukar jin tsoronSa! Ku yi riko da igiyar Musulunci mai aminci, ku sani lallai ne Shi (Allah) Ya tserar da ku daga wuta. Kuma lallai mala’ikan mutuwa ya kauda kai ne daga gare ku ya koma ga wasunku, kuma da sannu zai bar wasunku ya komo gare ku, don haka ku zauna cikin shiri! Mai hankali shi ne wanda yake taka-tsantsan da ransa kuma yake yin aiki domin abin da ke zuwa a bayan mutuwa. Kasasshe shi ne wanda ya bi son zuciyarsa, kuma ya rika gurace-gurace a kan Allah.
Ya ku Musulmi! Lallai mafi girman wa’azi shi ne mutuwa, wadda Allah Ya kaddara ta a kan wanda Ya so daga cikin halittu. Komai nisan ajalinsa da tsawon rayuwarsa sai mutuwa ta riske shi, ya mika wuya ga karfinta. Allah Madaukaki Ya ce: “Kowace rai mai dandanar mutuwa ce, sannan zuwa gare Mu ake mayar da ku.” (Ankabut:59).
Da Allah zai sanya dauwamma ga wani daga cikin halittunsa da ya kasance annabawanSa masu tsarki da manzanninSa mukarrabai ne. Kuma da wanda zai fi su cancantar haka shi ne zababbe daga cikin zababbunSa (Annabi Muhammad SAW), amma hakan bai yiwu ba, sai ma Ya shaida masa cewa: “Lallai ne kai mai mutuwa ne, kuma lallai su ma masu mutuwa ne.” (Zumar:30).
Mutuwa tilas ne babu makawa daga gare ta, kuma ba a guje mata, za ta riske mu a cikin gidajenmu da kan duwatsu da sararin sama da karkashin ruwa. Mala’ikun da ke cikin sama ma ba su tsere mata, haka mala’ikun da ke kasa. Babu wani mutum ko aljani ko dabba da zai tsere mata, koda ta kasancewa a cikin gidajen masu tsaro da dogayen katanga, “Duk inda kuka kasance mutuwa za ta riske ku, koda kuna cikin gidaje masu tsaro.”
Da ana kubuta daga mutuwa da mutum ya ba da jikinsa da karfinsa da dukiyarsa da wadatarsa da iko ko mulkinsa da abin da ya mallaka domin ya kubuta daga gare ta. Abin ya yi girma ga mutane ba su hankalta. Idan ba haka ba, ina Adawa da Samudawa? Ko ina Fir’auna ma’abucin turaku? Ina Kisrori da kaisarori? Ina manyan jabbaran masu mulki? Mutuwa ba ta jin tsoron kowa kuma ba ta barin kowa. Tana dauke jariri daga bakin nonon uwarsa. Tana auka wa matashi saurayi ko mai karfi da jarumtaka ta yi galaba a kansa.
Ya ku mutane! Sha’anin mutuwa a bayyane yake kuma a fili. Gurbinta sirri ne daga cikin asirrai wadanda suke zama abin lura ga masu hankali. Ta girgiza tare da shan kan hankulan mutane, ta bar masana falsafa da likitoci suna ta kai-kawo cikin rudu ba su gano sirrinta ba. Tsayawa bincike a kan mutuwa bata ce mabayyaniya da bala’i mai girma. Babu mai mantawa da ita face ya yi dagawa, babu mai gafala daga gare ta face tababbe, kuma ita ba ta da magani. Ba a kauce mata, sai dai mutum ya rika tuna fadin Allah Madaukaki: “Rai bai san abin da zai aikata gobe ba, kuma bai san a wace kasa zai mutu ba. Lallai ne Allah Masani ne Mai ba da labari.” (Lukman:30).

Huduba ta Biyu:
Ya ku Musulmi! Ya kamata kowane Musulmi ya rika tuna wasu darare biyu, daren da yake zaune a gidansa tare da iyalinsa da ’ya’yansa yana mai jin dadi da lafiya, yana dariya da ’ya’yansa yana yi musu wasanni suna yi masa wasanni da kuma daren da ke bin wannan, lokacin da mutum yake cikin wannan jin dadi, yake jin dadin lafiyarsa, yake ni’imtuwa da ni’imar lafiya, yana ji da karfi da samartakarsa, kwatsam sai mutuwa ta zo masa, ta tafi da shi ba tare da ya shirya ba. Kan haka ne Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku yawaita tuna mai rusa jin dadi (mutuwa)”
Ya ku Musulmi! Lallai muna da abin koyi mai kyau daga rayuwar magabatan kwarai, abin koyi mai dadi. Hakika sun kasance suna yawaita tuna mutuwa hatta a lokacin wadata da yalwa da jin dadi. Wannan yana dada karfafa su ga dada yin da’a ga Allah da guje wa saba maSa.
Wasu mutane sun ce: “Mun shiga wurin Adda’us Sulamiy don mu gayar da shi kan rashin lafiyar da ya rasu a cikinsa, sai muka ce masa: Yaya jiki? Sai ya ce: “Mutuwa ta zo min har wuya, ga kabari a gabana, kuma kiyama ce wurin tsayuwana, gadar Jahannama ce kawai ta saura ban san me za a aikata da ni a kanta ba.” Sannan ya yi kuka mai tsanani har ya suma. Da ya farka sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka yi min rahama, Ka sassauta min kan abin da nake tsoro a kabari da kuma tafiyata ga mutuwa. Kuma Ka yi min rahama a yayin tsayuwata a gaba gare Ka, ya Mafi rahamar masu rahama.”
Almazini ya shiga wurin Imam Shafi’i yana jinyar da bai tashi ba, sai ya ce masa: “Yaya jiki ya Abu Abdullahi?” Sai ya ce: “Na wayi gari Dinari bai da amfani, na wayi gari mai rabuwa da ’yan uwana, mai haduwa da mugun aikina, mutuwa tana kaina da takubbanta, kuma mai bijirowa ga Ubangijina Madaukaki. Kuma ban sani ba, shin ruhina zai wuce ne zuwa ga Aljanna, in yi masa murna ko kuwa zuwa ga wuta in yi masa jaje!”
To, yake rai, mai bin dajin son zuciya! Ki bar dajin wannan tunani na sa’a daya, ana tunatar da ke cewa lallai jin dadin gajere ne, ukuba kuma mai tsawo ne. Abin mamaki! Mai jin dadi yana sayan sha’awa ta sa’a daya cikin wahala da damuwa. Sabon sa’a daya amma mutum zai yi nadamar da bai yi ba, da yawa rai zai kaskanta a bayansa! Da yawa rai kan yi tsatsa saboda shi! Hawaye ya zuba saboda tuna shi! Allah Ya yi mana tsari gaba daya daga gafala da mummunar makoma a cikin dukiya da iyali da ’ya’ya.
Ya bayin Allah! Ina fadin abin da kuke ji ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku da kuma sauran Musulmi daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne, Mai jin kai.