Mutuwa rigar kowa (2)

Kamar yadda muka soma ambata a baya, a can da ne ake maganar agola, in an yi mutuwa wato a lokacin da mahaifiya ta rabu da miji ko kuma ya rasu, ita kuma ta sake aure, ‘ya’yan za su kasance tamkar ‘ya’yan sabon maigidan da suka samu kan su a ciki, wato inda ta koma […]

Mutuwa rigar kowa (2)
Mutuwa rigar kowa (2)

Kamar yadda muka soma ambata a baya, a can da ne ake maganar agola, in an yi mutuwa wato a lokacin da mahaifiya ta rabu da miji ko kuma ya rasu, ita kuma ta sake aure, ‘ya’yan za su kasance tamkar ‘ya’yan sabon maigidan da suka samu kan su a ciki, wato inda ta koma da sabuwar rayuwa. In kuma wata sabuwar mutuwar ko sakin suka sake ratsawa, dorawa kurum za a yi, tsoffaffin agola (wato yaran da aka zo da su daga wani gida) su suke komawa sabbabbin agola a wani gidan. Su kuma sababbin agola, wato wadanda mahaifiyar ba ta samu damar sake auren ba, za a ga sun samu sabon matsuguni, wato masu kulawa da su ko a wani sabon gida, nesa da su ko kuma a tsakanin kawunnai da goggonnai da innoni da babanni, wadanda ga su nan birjik. A cikin irin wannan yanayi wasu yaran ma ba su iya tuna rashin da suka yi, in ba na zahirin rashin ganin iyayensu ba. A cikin irin wannan tsari, rayuwa tafiya take kamar ba a samu tuntube ba. Yanzu fa? Abubuwan tuni sun canza!

Yanzu barazanar da ‘ya’yan da aka saki iyayensu ko iyayensu suka rasu ko kuma wadanda iyaye, musamman mata da suka rasa mazajensu ke fuskanta bai wuce na gaba kura, baya siyaki ba. Ba wai ana kukan rashin wanda ya rasun ba ne, ana kukan yadda rayuwa za ta kasance bayan ‘yan kwanaki da rabuwa da jigo ko madauki na ryuwar yau da kullum. Ba kuma wani abu ke jawo hakan ba, sai ganin cewa addu’ar uku ko bakwai ko 40 ga matan da suka rasa mazaje ko ‘ya’yan da suka rasa iyaye ta kasance tamkar wani dabam da ke tarwatsa rayuwar iyalin da aka bari a baya. Bama na rashin sanin madafa dangane da jagorancin gibin da aka bari. Bama na rashin sanin ina kuma za mu dosa (ga ‘ya’yan da aka bari) dangane da ciyarwa da tufatarwa da kuma matsuguni. Banda na kisan mummuke da ‘yan uwa da abokan arziki za su shiga yi, ganin cewa idon da ke sa su yin abin da suke yi, yau ya rufe, ba mai ganin sa balle a yi domin sa.

A irin wannan yanayin rayuwa sai ka ji mutane na cewa ai mutuwa ta tona asirin mamaci ko wadanda aka bari. Lallai kuwa za mu iya cewa an yi tonon silili, amma mamaci ne aka yi wa tonon sililin ko aka bayyana asirin da ke turbude? Shin ina ruwan mamaci da hargidiballen da ke faruwa a duniya a lokacin da yake kwance a cikin makabarta? Ina ruwan mamaci da rashi ko kunci ko damuwar da iyalin da ya bari a baya suke ciki? Ina ruwan sa dangane da kai-kawo da ake ta yi dangane da dukiyar da ya bari? Ina ruwan sa tun da shi bai da katabus a cikin wannan harka! Ina ruwan sa da jin kunya ko kuma damuwa dangane da halin da na bayan da ya bari ke ciki? Ina ruwan sa!

Ke nan za mu iya cewa wadanda ke da ruwa da tsaki a cikin wannan kwamacala, su ne wadanda ke a doron kasa ne. Wadanda ke shakar iska ko kuma suke wandaka da dan wa’adin da ya rage musu a doron kasa, ciki kuwa har da wadanda mamatan suka bari a baya da makusanta.

Me ya sa na ce? Kwakkarar hujjar da nake takama da ita ba ta wuce ganin irin abin da ke faruwa ba a lokacin da aka samu rashi a tsakanin al’ummarmu, musamman a wannan zamani da muke ciki. Yau mutuwa tonon asirin ‘yan uwa ce da makwabta da abokan hulda da kawaye. Yau mutuwa ba wanda take yi wa tonon silili irin na kusa da mamata, wadanda a lokacin da mamatan ke raye ba su kula da halin da suke ciki ba. Ba su ma damu da halin da suke cikin ba, in sun sani, domin matsalolin ba nasu ba ne, na su mamatan ne kafin su isa matabbata.

Bari mu yi gwari-gwari domin a gane inda muka dosa. Wa ya fi jin kunya ko aka tona wa asiri irin wanda dan uwansa ko abokinsa ko makwabcinsa ya yi wata da watanni, yana fama da cuta, ba ya lafiya, ya nemi taimakon zuwa asibiti ko na shan magani, amma a yi watsi da shi, domin shi Allah bai huwace masa ba, amma da zarar cutar ta warke, mamatan suka shuri birji sai ka ga ‘mataimaka’ sun kunno kai. Mai kawo abinci na kawo wa. Mai kawo abin sha na kawowa. Mai shimfida tabarmi na shimfidawa. Mai guzurin magunguna domin ‘ya’yan mamata na yi. Mai kukan karya na yi, wai an yi rashin dan uwa ko aboki ko makwabci, alhali ana iya cewa irin wadannan gwanjon mutane suna daga cikin azara’ilai masu daukar rai na wadannan mamata!

Wa ya fi jin kunya a tsakanin mamatan da suka rasu da haushin ‘yan uwa da abokan arziki da makwabta da suka bar mamata cikin kuncin talauci da damuwa. Suna ciyar da iyalansu da kyar a tsawon rayuwa, amma da zarar aka ce an koka, an yi rashi, ka ga gida ya cika, ya fantsama da mutane da abinci da abinsha. Buhunan shinkafa! Kwandunan kayan miya! Garewanin man gyada ko man ja! Tufafi domin yara da matan da aka bari! Kai a takaice in da za a yi zaman makokin shekara da shekaru, wadanda mamatan suka bari a baya ba za su koka ba, domin kullum rana ta Allah abinci da abinsha da sauran kayayyakin more rayuwa ba sa kadan.

Wa ya ji kunya in ba mu da mamatan suka bari a baya ba, da muka kasa taimakawa ko agazawa a lokacin da taimakon ko agazawar ke da muhimmanci? Wa ya fi jin kunya in ba mu ba da yanzu muke ta habba-habba da kokarin taimaka wa, alhali shi ma na ‘yan kwanaki ne? Kwana uku, kila bakwai, in an dade 40, ka nemi mutane sama ko kasa, an bar iyalan mamata cikin damuwa da kunci, bayan an lasa musu zuma a baki, an kuma bar su da jangwam! Wa mutawa ta yi wa tonon silili? Ba dai mamata ba! Ba kuma iyalan mamatan ba! Wa? Ni da ke da shi da kai da ita da su da ku; mu duka baki daya da muka ki yin abin da ya dace a lokacin da ya dace! Fakat!