Mutuwar Darakta Saleh AGM ta jijjiga Kannywood
Muturwar fitaccen darakta Saleh AGM ta jijjiga masana’antar fina-finan Hausa. Marigayin ya mutu ne a ranar Asabar sakamakon hadarin mota a lokacin da yake kan hanyarsa ta koma wa Maiduguri daga Abuja, bayan ya kammala daukar fim dinsa mai suna ‘Mallaka Min Dukiyarki’ Wata majiya ta ce motar marigayin ta fada cikin wani rami ne […]
Muturwar fitaccen darakta Saleh AGM ta jijjiga masana’antar fina-finan Hausa.
Marigayin ya mutu ne a ranar Asabar sakamakon hadarin mota a lokacin da yake kan hanyarsa ta koma wa Maiduguri daga Abuja, bayan ya kammala daukar fim dinsa mai suna ‘Mallaka Min Dukiyarki’
Wata majiya ta ce motar marigayin ta fada cikin wani rami ne a lokacin da yake tuki, hakan ya sanya ta rika wuntsulawa a karshe ya rasu bayan ya ji munanan raunuka da suka haifar da zubar jini sosai.
Fim din wanda ya hada da jarumai kamar su Yakubu Muhammad da Ali Nuhu da Rahama Sadau da Tijjani Faraga da Rabi’u Rikadawa da Sadik Sani Sadik da sauransu, marigayin ne ya rubuta shi, ya kuma ba da umarni.
George Onmonya Daniel abokin marigayin ya ce mutuwar ta jijjiga shi.
“Duk lokacin da Saleh AGM ya zo Abuja to a gidana yake sauka, ko a kwanakin baya da ya zo Abuja yana neman wuraren da zai dauki fim dinsa mai suna ‘Mallaki Min Dukiyarki’ a gidana ya zauna. Na je wurin da ake daukar fim din, har na tattauna da Ali Nuhu da Yakubu Muhammad. Jiya (Juma’a) da misalin 11:29 na dare muka yi magana da shi ta waya, a lokacin barci ya fara kama ni, ashe sallama na yi da shi. Mutuwarsa ta jijjiga ni, Allah Ya ji kansa.”
Rahama Sadau ta ce sai ta ji kamar mafarki take yi da aka fada mata mutuwar daraktan.
“Ina daya daga cikin jaruman da ke fim din ‘Mallaka Min Dukiyarki’, ana cikin daukar fim din mun yi wasa da dariya sosai, lokaci zuwa lokaci yakan zolaye ni, na karanta labarin mutuwarsa a shafin twitter ne, na kadu sosai. Na ji kamar a mafarki, sai na ce ko dai wasa ne kamar yadda aka saba yi wa ’yan fim, amma daga baya na bincika sai na tabbatar da mutuwar.” Inji ta.
Yakubu Muhammad ya ce za a dade kafin a cike gibin da marigayin ya bari ba, domin ya san aiki, kuma yana gudanar da harkokinsa bisa tsari.