Mutuwar dogarai 12 ta girgiza Hadeja -Sakataren Sarki

Sakataren Mai martaba Sarkin Hadejiya, Alhaji Maina Kawu Hadejiya ya bayyana wa Aminiya cewa rasuwar dogaran masarautar Hadejiya babban rashi ne matuka wanda masarautar ba ta taba yin irinsa ba. Alhaji Maina wanda ya bayyana haka lokacin da wakilinmu ya tuntube shi a game da rasuwar dogaran, ya ce daga cikin wadanda lamarin ya rutsa […]

Mutuwar dogarai 12 ta girgiza Hadeja -Sakataren Sarki

Mai Martaba Sarkin Hadeja, Alhaji Adamu AbubakarSakataren Mai martaba Sarkin Hadejiya, Alhaji Maina Kawu Hadejiya ya bayyana wa Aminiya cewa rasuwar dogaran masarautar Hadejiya babban rashi ne matuka wanda masarautar ba ta taba yin irinsa ba.
Alhaji Maina wanda ya bayyana haka lokacin da wakilinmu ya tuntube shi a game da rasuwar dogaran, ya ce daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai babban direban Sarki, wanda ake wa lakabi da Koli Direba da dankura dogari da Sarkin Dogarai da Galadiman Dogarai da wani dogari da ake wa lakabi da Na Ringim da Manu mai hoto da Sarkin Lema Maje. Masarautar Hadejiya ta fada cikin juyayi a ranar Litinin din nan da ta gabata a sakamakon mutuwar wadannan dogaran Sarkin Hadejiya guda 12 da suka rasa rayukansu a sakamakon taho-mu-gama da motarsu ta yi da wata tankar man fetur a wani gari da ake ce wa Wadugur da ke karamar Hukumar Ringim.
Kusan dukkan dogaran da suka rasa ransu tsofaffi ne, wadansu daga cikinsu ma tun zamanin Sarki Abubakar Maje suke aiki a fadar, lamarin da ya sa sarkin na Hadejiya a cikin mawuyacin hali ta yadda idan aka yi masa gaisuwa baya magana sai  dai ya yi jinjina da hannu, wani lokaci kuma aga zubar  da hawaye saboda juyayin halin da dogaran nasa suka fada.
Bayanai daga fadar ta Hadyejia sun tabbatar cewar wadannan dogaran  sun  rasu ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa tashar jirgin sama ta Malam Aminu Kano domin tarbar Sarkin lokacin da ya dawo  daga kasashen waje.
Shi kuwa Gimba Bello Auyo da yake karin bayani cewa ya yi, a ranar da aka zo musu da labarin rasuwar dogaran nan sai garin Hadejiya ya yi tsit, ‘yan kasuwa suka rufe rumfunansu, yayin da ma’aikata kuma komai ya tsaya cik, “lamura har zuwa yau din nan sun dagule a garin Hadejiya, kowa  ka gani yana tafiya ne jikinsa babu karfi.’’
Wata mata da take da dangantaka da Sarkin Dogaran na Hadejiya, watau Hajiya Adama Ibrahim, ta ce Sarkin Dogarai mutum ne mai hakuri matuka gaya, ba shi da saurin fushi kamar yadda wadansu dogarai suke da shi. Ta ce mutuwarsu ta girgiza mutane da dama a garin, domin ba karamar asara ‘yan uwa da abokan arziki suka yi ba, saboda mutane ne da suke zaune lafiya da jama’a.
Wani wanda hadarin ya faru a gabansa, Malam Abubakar Ramadan ya ce a lokacin da hadarin ya faru sun ji karar fashewar wani abu ne kamar bom, kasancewar a yankin sun san karar bom sakamakon hare-haren bam da wadansu suka kai garin na Ringim, sai suka kai agaji ga wadanda abin ya shafa da  suka je wajen babu yadda za su iya taimaka musu saboda kofar motar a kulle take kuma ga wuta ta kewaye su sakamakon taho-mu-gama da suka yi da tankar.
Wurin hatsarin da Dogarwan sarkin Hadejia goma sha biyu suka rasa rayukansuWani dogari da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce daga cikin dogaran 12 ba a ga gawar mutum guda ba, an nemi gawarsa ba a ganta ba, ya ce batan gawar wannan mutum ta kara tayar da hankalin al’ummar masarautar ta Hadeja.
Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a fadar Mai martaba Sarkin na Hadeja.