Mutuwar mahaka ma’adinai 200: Turkiyya ta ayyana zaman makoki na kwana uku

Gwamnatin kasar Turkiyya ta ayyana zaman makoki na kwana uku a kasar bayan da ma’aikatan hakar ma’adanai fiye da 200 suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ya haddasa gobara a wata mahakar kwal da ke yammacin kasar.daruruwan ’yan uwa da dangin wadanda lamarin ya rutsa da su cikin damuwa suka taru a kusa da […]

Mutuwar mahaka ma’adinai 200: Turkiyya ta ayyana zaman makoki na kwana uku
Mutuwar mahaka ma’adinai 200: Turkiyya ta ayyana zaman makoki na kwana uku

Gwamnatin kasar Turkiyya ta ayyana zaman makoki na kwana uku a kasar bayan da ma’aikatan hakar ma’adanai fiye da 200 suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ya haddasa gobara a wata mahakar kwal da ke yammacin kasar.
daruruwan ’yan uwa da dangin wadanda lamarin ya rutsa da su cikin damuwa suka taru a kusa da mahakar da ke garin Soma yayin da ma’aikatan ceto ke zakulo gawarwaki da mutanen da suka ji raunuka.
Da dama daga cikin mamatan sun mutu ne sanadiyyar shakar gubar sinadirin Carbon Monodide bayan fashewar wani abu mai matukar karfi da ke karkashin kasa.
Wakilin BBC ya ce fashewar abin ta faru ne kilomita biyu a karkashin kasa, lamarin da ya janyo katsewar lantarki tare da toshewar hanyar shakar iska ga mahakan.