Mutuwar marasa lafiya ta sa an rufe asibitin kudi a Kano

Gwamnatin jihar ta gano yadda ake wasa da rayukan marasa lafiya a asibitin.

Mutuwar marasa lafiya ta sa an rufe asibitin kudi a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani asibitin kudi sakamakon rahoton mutuwar wasu mutum biyu da aka samu cikin watanni shida a asibitin.

Hukumar Kula da Asibitocin Kudi ta Jihar (PHIMA) ce ta bada umarnin rufe asibitin asibitin mai suna ‘Green Olives Hospital’ da ke Sabon Titin Tal’udu a Karamar Hukumar Gwale,

Shugaban hukumar, Dokta Usman Tijjani Aliyu, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, hukumar ta gano yadda ake wasa da rayukan mutane a asibitin.

“Mun gano yadda likitoci da sauran ma’aikatan asibitin ke wasa da rayukan marasa lafiya.

“Sannan ba a cike takardar yarjejeniya kafin yi wa mara lafiya aiki, wanda hakan ya saba da dokar aikin likitanci,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Dokta Adamu, ya roki jama’a da su rika kokarin kai rahoton ire-iren asibitin da ke aikata irin hakan a fadin Jihar.

Kazalika, ya ba da tabbacin cewar za su tsaya tsayin daka don tabbatar da an hukunta wanda aka cafke a asibitin don girbar abin da suka shuka.

Ya kuma ce hukumar za ta ci gaba da hada gwiwa da masu ruwa da tsaki a Jihar don tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar.