Mutuwar mutum tara: Wadanda ‘yan sanda ke tuhuma sun ki amincewa da laifinsu
A kwanakin baya ne Rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi ta kame wadansu mutane da ake zargi da kashe mutane tara karkashin wata kungiya mai suna Babeli. Wadanda ake tuhuma, ana kuma zarginsu da hada kai da nufin kashe wasu mutune. ’Yan sandan sun zargi mambobin kungiyar nan ta Babeli da zartar da hukuncin kisa […]

A kwanakin baya ne Rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi ta kame wadansu mutane da ake zargi da kashe mutane tara karkashin wata kungiya mai suna Babeli.
Wadanda ake tuhuma, ana kuma zarginsu da hada kai da nufin kashe wasu mutune. ’Yan sandan sun zargi mambobin kungiyar nan ta Babeli da zartar da hukuncin kisa ga duk wanda suka kama da laifuka a yankin karamar Hukumar Warji da ke Jihar Bauchi ba tare da jiran doka ta yi aiki a kan masu laifin ba, zargin da wadansu daga cikin wadanda ake tuhuman suka musanta.
Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar, Kamal Datti Abubakar ya ce ’yan kungiyar suna yanke hukuncin kisa ne idan suka kama wanda ake zargi da aikata fashi da makami ko satar mutane. Ya ce sashen yaki da ’yan fashi da makami na rundunar ne suka kama wadanda ake tuhuma, bisa zargin suna kokarin kashe wani mutum.
Ya ce ’yan sanda sun dana tarko ga ’ya’yan kungiyar Babelin a lokacin da suka yi yunkurin kai farmaki ga wasu jama’a a kasuwar Warji a wannan ranar da kuma kokarin neman hllaka wani mutum mai suna Ya’u Nafada da ke kauyen Lafiya, a nan karamar Hukumar Warji.
Sai ya bayyana sunayen wadanda aka kama kuma suke zargi da suka hada da Ado Hamza dan shekara 35, wanda kuma aka fi saninsa da suna ‘Dawa Ado’ da ke zaune a kauyen Rumba, Idris Alhaji Hamza daga kauyen Wuro Mango, Bala S. Aska da kuma wani tsoho mai suna Ardo Abdu dan shekara 67 da ke kauyen Kaden Kanawa.
Kamal ya ce dukkan wadanda suka Kaman suna daga cikin wadanda ake zargi da hada kai wajen kashe jama’a a kauyuka daban-daban, wanda adadin da rundunar ta gabatar ta kuma ce ’yan Babeli sun kashe su sun kai mutane 9, sai ya gabatar da sunayen wadanda ake zargin sun kashe da suka hada da marigayi Ori Mai’awaki da ke kauyen Gabanga, Boderi Ibbi mazaunin kauyen Ranga, Musa Beti daga kauyen Tiyin, Mota Aru daga kauyen Aru, da dangairu Haruna da ke zama a kauyen Aru, Pijo Aru shi ma daga Aru, sai kuma Umaru Muda daga kauyen Muda, sai marigayi Shugaba Dajji mazaunin kauyen Yayari da kuma Idi Sale da ke yankin Tudun Wada a Karamar Hukumar Warji.
Kakakin ya ce za su gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu da zaran sun kammala bincike.
Wadansu daga cikin wadanda aka kama dangane da kisan jama’a sun musunta zargin. “Ni sunana Hardo Abdu, ni mazaunin karamar Hukumar Warji ne. Ni gaskiya zargin da ake yi mani karya ne, babu abin da na yi aka kawo ni nan. Ni zargina ake yi wai ni dan kungiyar Babeli ne, ni kuma babu abin da ya hada ni da kungiyar Babeli, ba na yinta kuma ba na da alaka da ita wannan kungiyar. Daga cikin wadanda aka kawo mu nan, sun tabbatar ni ba na daga cikinsu, amma sun ci gaba da tsare ni yau kwanana goma 11 ina tsare a nan.”
Hardo ya ce “Su ’yan kungiyar Babeli suna tafiya ne da bindiga, adduna da kuma sanduna, suna tafiya ne da shirinsu da zarar suka kama mai garkuwa da mutane sai su yanke masa hukuncin kisa kai tsaye.
“Suna shiga cikin karamar hukuma kuma ita karamar hukumar ta san da su, to mu mene ne muka isa mu ce tun da suna shigowa cikin kasuwa, suna kuma shiga cikin karamar hukuma? Ka ga mu babu abun da za mu iya cewa tun da su manyan jama’armu sun gane su, don haka mu babu abun da za mu iya cewa. Matakinmu dai shi ne mu sanar da hukuma, hakimi ko dagaci dukkaninsu sun sani me za mu ce musu.”
Shi ko shugaban wani yanki na kungiyar Babeli da aka kamo mai suna Ado Dawa, ya ce “na zo nan ne a kan kungiyar Babeli. Har ga Allah mu muna tafiya a kungiyance, hidimar kungiyar da muke tafiya a kai, mu dai an fara ta ne a yankinmu. A yankinmu din nan kuma kungiyar ta kasu kala-kala, akwai Ganjuwa akwai Jigawa, sukan shigo mu lokaci bayan lokaci.”
Ado ya ce “mu a yankinmu na Warji idan muka kama masu laifi, akwai wani soja mai suna Manjo Uba, shi muke kai masu laifi, shi yana rikon aikin soja a Ningi da Warji ne. Ya zuwa yanzu mu mun kama mutane uku kuma mun mika a hanunsa.”