Mutuwar Paul Walker ta girgiza masoyansa

A ranar Asabar da ta gabata ce shahararren jarumin fim din ‘Fast and Furious,’ Paul Walker ya gamu da ajalinsa a sakamakon hadarin mota.Paul, dan shekara 40, ya rasa ran nasa ne, a yayin da motar da abokinsa yake tukawa, wacce kuma yake cikinta ta gamu da mummunan hadari. Motar, kirar ‘Porsche’ ta fadi ne […]

Mutuwar Paul Walker ta girgiza masoyansa

A ranar Asabar da ta gabata ce shahararren jarumin fim din ‘Fast and Furious,’ Paul Walker ya gamu da ajalinsa a sakamakon hadarin mota.
Paul, dan shekara 40, ya rasa ran nasa ne, a yayin da motar da abokinsa yake tukawa, wacce kuma yake cikinta ta gamu da mummunan hadari. Motar, kirar ‘Porsche’ ta fadi ne kuma ta kama da wuta a kusa da zauren da ake gudanar da wani taron nema wa gajiyayyu tallafi.
Kamar yadda sanarwar hadarin ta bayyana a turakar mamacin a Facebook: “Tare da bakin ciki da alhini, muna sanar wa al’umma mutuwar Paul Walker ta hanyar hadarin mota, wanda ya faru, a yayin da yake tafiya zuwa halartar wani taron tallafa wa marasa galihu, wanda kungiyarsa ta tallafa wa gajiyayya ‘Reach Out Worldwide’ ta shirya.” Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Marigayin yana gidan gabar motar abokinsa, a yayin da hadarin ya faru, inda dukkansu biyun suka mutu. Muna yabawa da hakurinku, domin kuwa mu kanmu muna cikin alhini da jimami, a lokacin da labarin hadarin ya ishe mu. Muna godiya da addu’o’inku gare shi da iyalinsa, a yayin da suke cikin wannan mawuyacin yanayi.”
Matukin motar, wanda abokin Paul ne, sunansa Roger Rodas, wanda shi ne shugaban kamfanin ‘Always Ebolbing’ wanda ya kware wajen hada gasar tseren motoci kuma mallakin marigayin ne.
Tashar rediyo ta ‘TMZ’ ce ta fara ba da rahoton mutuwar dan wasan, inda ta ce motar da marigayin ke ciki ta kauce daga hanya ne, inda ta bugi wani turken kan hanya kuma ta kama da wuta. Ta ce al’amarin ya faru ne a daidai misalin karfe uku da rabi na yammacin Asabar da ta gabata.
Kamar yadda hukumar ’yan santa ta yankin ta bayyana yadda al’amarin ya faru, ta ce: “A lokacin da jami’an ’yan sanda suka halarci wurin hadarin, sun samu motar tana cin wuta, inda ’yan kwana-kwana suka yi hanzarin kashe ta kuma suka yi kokarin dauko mutane biyu da ke cikin motar, wadanda tuni sun mutu.”
’Yan sanda a unguwar Santa Clarita, inda hadarin ya faru, sun danganta tsananin gudu da direban ke yi a matsayin musabbabin afkuwar hadarin. Motar dai mai jan fenti, samfurin kirar ‘Porsche Carrera GT 2005’ ce.
Masoyan Paul Walker, wanda fitaccen dan fim ne kuma dan wasan tseren mota sun bayyana alhininsu da mutuwar jarumin nasu.