Mutuwar shugaban masu zaben Ooni ta haifar da takkadama

Mutuwar shugaban masu zaben sabon sarki a masarautar Ife, Obalufe na Iremo, Oba Solomon Folorunso Omisakin, ta bar baya da kura a kan batun zaben sabon Ooni na Ife da zai maye gurbin marigayi Oba Okunade Sijuwade wanda ya mutu watanni 3 da wucewa. Takaddamar da ta sake kunno kai a yanzu da shugaban masu […]

Mutuwar shugaban masu zaben Ooni ta haifar da takkadama
Mutuwar shugaban masu zaben Ooni ta haifar da takkadama

Mutuwar shugaban masu zaben sabon sarki a masarautar Ife, Obalufe na Iremo, Oba Solomon Folorunso Omisakin, ta bar baya da kura a kan batun zaben sabon Ooni na Ife da zai maye gurbin marigayi Oba Okunade Sijuwade wanda ya mutu watanni 3 da wucewa.

Takaddamar da ta sake kunno kai a yanzu da shugaban masu zaben ya mutu a ranar Alhamis ta makon jiya ita ce, batun yiwuwar zaben sabon Ooni ba tare da hannun shugaban masu zaben sabon sarki ba.
A wani bincike da wakilinmu ya gudanar, ya gano cewa mutuwar shugaban ta raba kawunan masarautar gida biyu, domin akwai masu hangen cewa, za a iya ci gaba da aikin zaben sabon Ooni a yanzu ba tare jiran nada sabon shugaban ba, a yayin da daya bangaren ke cewa, yin haka ya saba wa al’ada.
Har ila yau akwai jita-jitar cewa an yi amfani da guba ne wajen kashe shugaban masu zaben sabon sarkin saboda irin rawar da ya taka a kan batun amincewa da gidan sarautar Geisi a matsayin gidan da ya cancanta ya fito da ’yan takara masu neman hayewa bisa karagar wannan masarauta ta Ile-Ife tushen yarbawa wanda yin hakan bai faranta wa sauran gidajen sarautu uku ba. Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, bayan mutuwar shugaban, wanda shi ne na biyu a kan jerin sunayen manyan fadawan sarki, yanzu haka mutum na uku cikin wannan jeri wato, Lowa na Ife yana fama da rashin lafiya da ake danganta ta da yawan shekaru.
Da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da mutuwar mahaifinsa, babban dan marigayi Obalufe na Iremo, Yarima Omidiran Omisakin ya musanta jita-jitar cewa an yi amfani da magani ne wajen kashe mahifin nasa. Ya ce: “Babana ya mutu ne bayan wata ganawa da mahaifiyata da suka shafe minti 15 suna tattaunawa lami lafiya a ranar Alhamis ta makon jiya.”
A game da batun hanzarta binne gawar mahaifin nasa domin a samu damar nada sabon Obalufe da zai ja ragamar masu zaben sabon Ooni na Ife, sai Yarima Omidiran ya ce: “mahaifinmu ne ya mutu, babu wanda ya isa ya tilasta mu yin jana’izar gawarsa ba tare da mun shirya ba.” Ya yi tambayar cewa, yaya za a hanzarta binne gawar mahaifinmu ba tare da sanar da sauran ’yan uwa da ke zaune a kasashen duniya daban0daban ba?
Dangane da yiwuwar zaben sabon Ooni na Ife ba tare da an samu sabon shugaban masu zaben sabon sarki ba, ya ce: “Abun da na sani shi ne, mai rike da sarautar Obalufe na Iremo, shi ne jagoran masu zaben sabon Ooni da yake bayar da umarni da sanarwar mutuwar sarki da ambaton sunan sabon sarki. Ya za a yi zabe a Najeriya ba tare da hukumar zabe INEC ba?” inji shi.
Tabbatattun bayanan da wakilinmu ya jiyo mana sun nuna cewa, manyan fadawa a fadar Ooni na Ife a karkashin jagorancin Lowa na Ife, sun garzaya zuwa Osogbo babban birnin Jihar Osun a ranar Litinin da ta gabata, domin ganawa da Gwamnan jihar, Ogbeni Rauf Aregbesola a kan wannan babban al’amari mai rikitarwa.