Mutuwar shugabanta: Majalisar Taraba ta ayyana zaman makoki na yini biyu

Majalisar Dokoki ta Jihar Taraba ta ayyana zaman makoki na yini biyu don girmama marigayi shugabanta Mista Haruna Tsokwa wanda ya rasu a ranar Litinin da ta gabata. Wata sanarwa daga Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Adamu Tanko Maikarfi, ta umarci a yi kasa-kasa da tutar Najeriya a harabar majalisar a lokacin zaman makokin.Mutane na ci […]

Mutuwar shugabanta: Majalisar Taraba ta ayyana zaman makoki na yini biyu
Mutuwar shugabanta: Majalisar Taraba ta ayyana zaman makoki na yini biyu

Majalisar Dokoki ta Jihar Taraba ta ayyana zaman makoki na yini biyu don girmama marigayi shugabanta Mista Haruna Tsokwa wanda ya rasu a ranar Litinin da ta gabata.

Wata sanarwa daga Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Adamu Tanko Maikarfi, ta umarci a yi kasa-kasa da tutar Najeriya a harabar majalisar a lokacin zaman makokin.
Mutane na ci gaba da tururuwa zuwa gidan marigayin da ke Lasandi a garin Jalingo da kuma harabar majalisar domin mika ta’aziyyarsu kan rasuwar shugaban.
Iyalan marigayi Tsokwa sun bayyana shirye-shiryen binne gawarsa, inda suka nuna za dauke shi zuwa mahaifarsa Takum a ranar 27 ga Nuwamba bayan an yi wakokin yabo a ranar 26 ga Nuwamba, yayin da za a binne shi a ranar 28 ga Nuwamba.
Margayi Haruna Tsokwa ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jalingo, bayan ya hadu da hawan jini a ranar Larabar makon jiya.
Marigayin ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka hari ga ayarinsa ranar 19 ga Satumba a kusa da Keffi da ke Jihar Nasarawa a hanyarsa ta zuwa Abuja. Ya zamo daya daga cikin wadanda suke da hannu dumu-dumu a rikicin siyasar Taraba bayan da ya ki amincewa da wasikar da Gwamnan Jihar danfulani danbaba Suntai ya aike wa majalisar bayan dawowarsa daga jinyar wata 10 kan hadarin jirgin saman da ya rutsa da shi.
Marigayin mai shekara 47, ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya biyar.