Mutuwar ’yan mata 26 a Bahar Rum
Hankulan jama’a sun tashi ainun, ba ma a Najeriya ba kadai har da sauran kasashen duniya game da labarin rasuwar wasu ‘yanmata ashirin da shida, ‘yan asalin Najeriya wadanda shekarunsu ke kasa da ashirin, da aka ce an makure su har sai da suka marmace a kokarin da suke yi don ketara tekun bahar Rum […]
Hankulan jama’a sun tashi ainun, ba ma a Najeriya ba kadai har da sauran kasashen duniya game da labarin rasuwar wasu ‘yanmata ashirin da shida, ‘yan asalin Najeriya wadanda shekarunsu ke kasa da ashirin, da aka ce an makure su har sai da suka marmace a kokarin da suke yi don ketara tekun bahar Rum zuwa ci-rani a nahiyar Turai. Rahotannin da suka iso Najeriya daga Italy sun nuna cewa kafin a gano gawawwakinsu a cikin tekun sai da aka yi masu fade, sa’annan aka yi masu kisar gilla.
An dai ce an ajiye gawawwakin ‘yan matan masu shekaru goma sha hudu zuwa goma sha takwas ne cikin wani daki mai sanyi na wani jirgin yakin kasar Andalusiya, mai suna Cantabria, wanda kuma ke dauke da wasu ‘yan ci-rani guda dari uku da saba’in da biyar da suka hada da ‘yan Najeriya da Sanagal da Gambiya da kuma Sudan. Daga cikinsu akwai wasu mata guda casa’in, kuma takwas daga cikinsu na da ciki, hade da wasu yara hamsin da biyu. Tuni gwamnatin kasar Italiya ta yi jana’izarsu.
Wannan kadan ne daga cikin ire-iren bala’o’i da ukubar da ‘yan asalin kasashen bakar fata na Afirka ke afkawa ciki a kokarinsu na ketarewa zuwa kasar Italiya a nahiyar Turai yayin da suke ratsa tsakiyar Hamadar Sahara don gujewa daga talaucin da suke cewa na addabarsu a kasar nan. Ana yawan bayar da labarai marasa dadin ji game da haka wadanda suka hada da yadda ake takura wa ‘yan ci-ranin, da kuma yadda ake cin mutunci da zarafinsu har ma da gana musu mummunar azaba idan ba su yarda gungun marasa imani sun take su ba.
Kaman shekaru ashirin da suka wuce ‘yan ci-rani daga kasashen bakaken fatar nahiyar Afirka suka tsiri ficewa zuwa nahiyar Turai, kuma abubuwan da ke karfafa masu gwiwa don yin haka sun hada da yunwar da ake fama da ita a wasu kasashe hade da yake-yake da tashin-tashinar siyasa da talauci ko matsin tattalin arziki da illolin da rashawa ke haddasawa a garuruwansu. Mutane da yawa dai na ganin zuwa ci-rani kasahen nahiyar Turai, ta ratsa tsakiyar Hamadar Sahara da kuma Tekun Bahar Rum, babbar kasada ce ko kuma a ce sai da rai ne a banza.
A kwana-kwanan nan ma an samu ‘yan Najeriya da Ghana har guda arba’in wadanda kishin-ruwa da yunwa suka halaka a tsakiyar Hamadar Sahara aka kuma binne su a can. Haka nan kuma bini-bini kadan za a ga an komo da wasu daruruwan ‘yan Najeriya ranga-ranga, shiyyan-magashiyyan, bayan sun gama tagayyara a kokarinsu na ketare Hamadar sahara ko kuma Bahar Rum
Ya zama wajibi ga gwamnatin Tarayya ta magance matsalolin cikin gida da ke sanya mutane ficewa zuwa ci-rani a kasashen nahiyar Turai. Masu wannan gagarumar kasadar kan kashe sama da Dalar Amurka dubu biyar zuwa shida kafin su kai ga biyar bukatarsu ta isa kasar Turai; to amma idan haka ne wadannan makudan kudaden ba za su ishe su ba wajen fara wata sana’a a nan cikin gida idan aka yi canjinsu zuwa Nairarmu? Ashe ke nan ana iya yin kira ga kungiyoyin Hada kan kasashen Afirka da kuma ta kula da tattalin atzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS su kokarta wajen kawo karshen wannan al’amari mai ban takaici. Ya kamata su ma su dauki hannu daga kungiyar kasashen Turai da ke hana baki shiga kasashensu barkatai, su ma su inganta al’amura a kasashensu domin jama’arsu su daina ficewa daga cikin su.
Baicin haka nan kuma kasashen Turai sun bullo da wasu dabaru guda hudu don hana baki daga nahiyar Afirka kwarara cikin tasu nahiyar. Sun hada da rage taimako ko karfafa gwiwar bakin da ke shigowa kasashensu da kuma inganta sanya idanu akan iyakokin kasashensu don gano bakin haure, hana bayar da mafaka ga masu tsere wa matsalolin siyasa ko na tattalin arzikin kasashensu da kuma kara tsaurara matakan amincewa da bakin hauren da ke son shigowa kasashensu.
Dangane da samun nasara a wadannan al’amuran ne kungiyar kasashen nahiyar Turai ta kafa wani asusu na musamman domin taimaka wa kasashen Afirka dukufa kan magance al’amura da matsalolin da ke sa ‘ya’yansu firfucewa daga kasashensu suna kwarara cikin nahiyar Turai. Asusun kuwa na mayar da hankali wajen fitar da kudade don aiwatar da wasu tsare-tsare da aikace-aikace a kasashen nahiyar Afrika don kirkiro guraben ayyuka, ta yadda matasan da ke tsallakewa za su zauna a gida, su karu da haka sa’annan kuma a ci moriyarsu. Sauran ayyukan da ake yi da kudade daga asusun kuma suna taimakawa wajen ingantuwar harkokin mulki da na zamantakewa. Ta haka ne ake ganin za a samu abubuwan yi a kasashen nahiyar Afirka har ‘ya’yansu su zauna cikinsu, su kuma daina tunanin ficewa zuwa wasu kasashe ci-rani.
To, amma duk da cewa Najeriya na amfana daga irin waccan gudummawar da kungiyar kasashen nahiyar Turai ke samarwa, rashawar da ta yi katutu a kasar na hana ‘yan kasar cin gajiyarta, domin kuwa ba a amfani da kudaden bisa ga ainihin dalilan da suka sanya aka bayar da su tun can farko. Baicin haka ma yawancin masu zuwa nahiyar Turai ci-rani daga Najeriya ‘yan mata ne, wadanda ba su haura shekaru goma sha biyar ba, kuma babu abin da ke kai su can illa karuwancin da wasu marasa takawa ke yaudararsu, suna kuma daukar nauyinsu zuwa can wuraren da ake aikata badala. Ashe ke nan ana iya cewa ba fatara ko halin matsin tattalin arziki ko muzgunawar siyasa ce ke sa ‘yan-matan Najeriya ficewa kasar ci-rani a wasu kasashe ba, illa halayyar ‘yan Najeriya na lalaci da son na banza.
Ba nahiyar Turai ce kadai ba ‘yan Najeriya kan je don sana’ar karuwanci, har kasashen Larabawa da Saudiyya ma suna zuwa dangane da wanan mummunar sana’ar.
A yanzu hukumomin wadancan kasashen sun gano cewa abin da ke kai wasu mata kasar ke nan, ba yin ibada ba. Saboda haka nan hukumomin kasashen Larabawa sun dauki matakan tsananta tsaro da kuma hana irin wadancan mata shiga kasar har su aikata masha’ar da suke so. Darasin da ya auku ga wadancan ‘yan mata 26 da suka yi asarar rayukansu a banza, kan hanyarsu ta zuwa aikata aikin banza, ya isa ishara ga sauran mutanen banzan da ke sha’awar ficewa kasar don zubar da mutuncin Najeriya a banza.