Myanmar ta daure ’yan jaridar Reuters shekara 7
Wata kotu a Myanmar ta daure wadansu ’yan jarida 2 na Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters shekara bakwai a gidan yari bayan ta same su da laifin keta doka a yayin gudanar da aikinsu na bincike kan rikicin kabilar Rohingya. An kama Wa Lone da Kyaw Soe Oo, dukansu ’yan asalin Myanmar duk da cewa […]

Wata kotu a Myanmar ta daure wadansu ’yan jarida 2 na Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters shekara bakwai a gidan yari bayan ta same su da laifin keta doka a yayin gudanar da aikinsu na bincike kan rikicin kabilar Rohingya.
An kama Wa Lone da Kyaw Soe Oo, dukansu ’yan asalin Myanmar duk da cewa suna dauke da takardun izini da ’yan sanda suka ba su don gudanar da aikinsu.
’Yan jaridar sun musanta taka doka tare da zargin ’yan sanda da dana musu tarko.
Mutanen biyu sun shafe tsawon lokaci suna tattara hujjoji kan kisan da sojojin kasar suka yi wa wadansu mutum 10 a kauyen Inn Din da ke Jihar Rakhine kamar yadda Rediyon Faransa ya ruwaito.
Sun samu takardun izini daga ’yan sanda, amma aka kama su nan take kan mallakar takardun.
Ana kallon shari’ar ’yan jaridar a matsayin wani gwaji kan ingancin ’yancin fadin albarkacin baki a Myanmar. Tun a shekarar 2017 ake tsare da ’yan jaridar a gidan yari kuma dukansu na da iyalai da kanana yara.