n Kudancin Sudan ya auka wa asibitoci – kungiyar Likitocin agaji

kungiyar Likitocin agaji mara shinge, ta “Doctors without borders,’ sun bayyana cewa mayakan da ke fafatawa da juna a rikicin Kudancin Sudan sun fantsama da kai hari har cikin asibiti, inda suka sace muhimman kayan aiki, suka kuma halaka majinyata da ke kwance a asibitocin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.kungiyar Likitocin […]

n Kudancin Sudan ya auka wa asibitoci – kungiyar Likitocin agaji
n Kudancin Sudan ya auka wa asibitoci – kungiyar Likitocin agaji

kungiyar Likitocin agaji mara shinge, ta “Doctors without borders,’ sun bayyana cewa mayakan da ke fafatawa da juna a rikicin Kudancin Sudan sun fantsama da kai hari har cikin asibiti, inda suka sace muhimman kayan aiki, suka kuma halaka majinyata da ke kwance a asibitocin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
kungiyar Likitocin Agajin ts Medecins Sans Frontieres (MSF) ta bayyana cewa ayyukan kula da lafiya a irin wannan yanayi suna tattare da hadari, “ana kashe majiyata a kan gadon asibiti, da kona dakunan kula da marasa lafiya da sace kayan aiki, har a wani yanayin ma an lalata asibitin.” A garin Leer, wato mahaifar shugaban ’yan tawaye, Riek Machar, kungiyar likitocin ta ce an wawushe asibiti.
Kimanin mutum dubu 900 ne yaki ya tursasa su suka fice daga gidajensu, bayan da aka shafe watanni biyu ana fada tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin kasar, wadanda ke samun goyon bayan  Sojojin kasar Uganda, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.